An Ji Yadda N20,000 Ta Hana Wani Fitaccen Mawakin Najeriya Yin Karatun Jami'a
- Ice Prince ya bayyana yadda rashin iyaye ya zama ƙalubale ga rayuwarsa, har ya rasa gurbin shiga jami’a saboda N20,000
- Mawakin na Najeriya ya ce rayuwarsa ta dogara kacokan kan hukuncin Allah, domin ba shi da wani dangi ko mataimaki
- Ice Prince ya ce nasarar da ya samu a rayuwa hujja ce ta nuna cewa babu maraya sai raggo, kuma kalubale ba ya hana nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Mawaki Panshak Henry Zamani, wanda aka fi sani da Ice Prince ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta bayan rasuwar iyayensa lokacin yana ƙarami.
Ice Prince ya tuno lokacin da ya gagara samun gurbin karatu a jami’a saboda rashin N20,000 da zai biya kudin makarantar.
Ice Prince ya gamu da gagarin rayuwa
A wata hira a shirin ‘Listen’ podcast, da The Nation ta bibiya, Ice Prince ya bayyana yadda ya tashi a matsayin maraya tare da matsalolin da ya fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin ya bayyana cewa mahaifinsa ya rasu yana ɗan shekara 11, yayin da mahaifiyarsa ta rasu lokacin yana ɗan shekara 21.
"Ina so mutane su kalli rayuwata, su kuma ayyana a ransu cewa in har mutum maraya kamar ni zai iya yin nasara, to su ma za su iya tunkarar kalubalensu."
- A cewar mawaki Ice Prince.
Ice Prince Zamani ya ce ya yi ayyukan kaskanci da dama domin kawai ya tallafa wa kansa da 'yan uwansa da suka dogara da shi bayan rasuwar iyayensu.
N20,000 ta hana Ice Prince shiga jami'a
A cewar mawakin:
"Ba ni da uwa ko uba, kuma ni ɗaya ne a wajen iyayena. Rashin iyaye ya kasance ƙalubale mai girma a rayuwata."
"Duk nasarorin da na samu a rayuwa sun faru ne saboda taimakon Allah. Ba ni da wani uba ko uwar gida da nake dogara da su."
Na kan shafe makonni uku ina zaune a gida kowane zangon karatu saboda rashin biyan kudin makaranta. Ban je jami'a ba saboda rashin N20,000."
Mawakin ya ce duk wata fafutuka ta ganin ya hada N20,000 ta ci tura, yana ji yana ganin ya rasa gurbin karatu a jami'ar.
'Yan sanda sun cafke mawaki Ice Prince
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan sandan Legas sun cafke mawaki Ice Prince Zamani kan zargin ya lakadawa jami'in dan sanda dukan tsiya.
An rahoto cewa dan sandan ya tare mawakin ne da tsakar dare yana tuki babu lamba a motarsa, lamarin da ya kai mawakin ya daki jami'in da yi masa barazana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng