Ice Prince Zamani, Shahararen Mawakin Najeriya Ya Bayyana Darasin Da Ya Koya Bayan Sako Shi Daga Gidan Yari

Ice Prince Zamani, Shahararen Mawakin Najeriya Ya Bayyana Darasin Da Ya Koya Bayan Sako Shi Daga Gidan Yari

  • Ice Prince Zamani, shahararren mawaki gambara na Najeriya ya shaki iskar yanci bayan shafe kwanaki a gidan yarin Kiri-kiri a Legas
  • Rundunar yan sandan Jihar Legas ta kama Ice Prince ne a ranar 2 ga watan Satumba kan zarginsa da duka da sace dan sanda bayan kama shi yana tuka mota babu lamba
  • Ice Prince, bayan cika ka'idojin belinsa ya fito daga gidan yari ya kuma wallafa rubutu a shafinsa inda mutane suka rika yin sharhi

Jihar Legas - Fitaccen mawakin Najeriya, Ice Prince Zamani, ya ce lallai 'kudi ba zai iya siya siyan yanci ba' bayan an sako shi daga gidan yarin Ikoyi

An kama mawakin ne kan zarginsa da sace wa da dukan yan sanda a farkon wannan watan.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Ice Prince Zamani
Shahararren Mawaki, Ice Prince Zamani, Ya Yi Magana Bayan An Sako Shi Daga Gidan Yarin Kiri-Kiri. Hoto: @BenHundeyin.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawakin, ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter bayan sakinsa inda ya ce:

"Kudi ba zai iya siyan yan ci ba".

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya yi magana kan kama Ice Prince.

Hundeyin, a shafinsa na Twitter ya ce:

"Misalin karfe 3 na dare, an tsare @Iceprincezamani saboda tuki ba tare da lamba ba. Ya amince a tafi da shi caji ofis."
"Daga nan, ya sace dan sanda a motarsa, ya duke shi, kuma ya yi barazanar zai jefa shi cikin rafi. An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau."

An saki mawakin bayan ya cika ka'idojin belinsa a ranar Alhamis.

Lauyan Ice Prince, Folarin Dalmeida, ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hukumar PSC, Musiliu Smith Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

"An cika ka'idojin belinsa, kuma an sake shi jiya."

Martanin wasu mutane a Intanet

@misterkendy1 ya ce:

"Barka da dawowa Sarki ICE"

@Damie290 ya rubuta:

"Baba ya ga abin karfafa gwiwa da idonsa"

@chenemi15 ya ce:

"Ya ga 'shege' a hannun mutanen kenan ko?"

@hulkofafrica ya rubuta:

"Kamar an sako tsintsu daga kejin".

@Richiebankz90 ya ce:

"Idan ka ga dama nan gaba ka sake zuwa ka yi wa yan sanda garaje."

@MukhtarAdam02 ya ce:

"Allah ya kiyaye gaba".

@vino_val cewa ya yi:

"Lallai kudi ba zai iya siyan yanci ba, mun goda Allah ka dawo lafiya, ka koyi darasi da karfi da yaji.."

@EmperorTwiTs ya ce:

"Ina taya ka murnar samun yanci. Ka koyi darasi.

"Mu rika dage wa mu zama yan kasa na gari dukkan lokaci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel