Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau

Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau

- A makonni biyu da suka gabata rahoton mutuwar shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau ya karaɗe kafafen watsa labarai

- Bayan bayyanar rahoton mutuwar tasa, wasu na ganin ai wannan ba shine karo na farko da ake cewa ya mutu ba

- Akwai wasu manyan dalilai biyar da suka tabbatar da cewa rahoton mutuwar Sheƙau gaskiya ce

A kwanakin baya ne labarin mutuwa Abubakar Shekau ya karaɗe kafafen watsa labarai a Najeriya.

Sai dai duk wannan yayata labarin da aka yi, gwamnatin Najeriya da kuma ƙungiyar Boko Haram ba su ce uffan ba game da mutuwar Shaƙau ɗin.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 33, Sun Yi Awon Gaba da Dabbobi da Dama a Kaduna da Zamfara

Amma a kwanan nan rahoton mutuwar ya ƙara ƙarfi bayan ƙungiyar ISWAP da ta ɓalle daga Boko Haram ta fitar da sanarwa cewa ta Kashe Sheƙau.

BBC ta zanta da wani masanin al'amuran tsaro kuma ma'aikaci a cibiyar Tony Blair dake Burtaniya, Bar. Bulama Bukarti, inda ya lissafo dalilai 5 da suka tabbatar da cewa Sheƙau ya sheƙa lahira.

Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau
Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau Hoto: dailysabah.com
Asali: UGC

1. Rahoton mutuwar ya fara fitowa daga jaridu

Bulama yace dalili na farko shine labarin kashe Abubakar Sheƙau ya fito ne daga wasu jaridun Najeriya waɗanda keda alaƙa da hukumomin tsaron Najeriya.

A rahoton jaridun sun bayyana cewa jami'an tsaro sun yi kutse cikin wayoyin kwamandojin ISWAP, inda suka ji cewa sun kashe Sheƙau.

2. Makusantan Boko Haram da ISWAP sun wallafa labarin

Na biyu, masanin yace jaridu masu kusanci na kusa da ƙungiyoyin ta'addanci na Boko Haram da ISWAP sun wallafa labarin mutuwar.

Ya ƙara da cewa jaridun sun yi cikakken bayanin yadda suka tuntuɓi majiyoyin su na ɓangarorin biyu, kuma suka tabbatar musu da cewa Abubakar Shekau ya mutu.

3. Mutane masu kusanci da Boko Haram a Jihar Borno

Na uku, Br. Bulama yace wasu mutane a yankin arewa maso gabas sun tabbatar da mutuwarsa, kuma rahotanni sun nuna cewa mutanen suna da majiyoyi daga Boko Haram.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya

4. Har yanzun Abubakar Sheƙau bai fito ya ƙaryata ba

Masanin yace wani babban dalilin kuma shine yadda aka ji shiru shugaban Boko Haram ɗin bai fito ya ƙaryata mutuwar tasa ba kamar yadda ya saba yi a baya.

5. ISWAP da aka ruwaito ta kashe shi ta tabbatar

Dalili na ƙarshe wadda yafi ƙarfi inji Bar. Bulama shine ƙungiyar ISWAP ta fito ta tabbatar da ta kashe Sheƙau.

A ranar Jumu'a ISWAP ta fitar da wata sanarwa cewa ta kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau, tare da zayyana yadda ta sheƙe shi.

A cewar Bulama waɗannan dalilan kaɗai sun isa su tabbatar da mutuwar Sheƙau, ya kuma ƙara da cewa ISWAP sun bayyana cewa suna cigaba da yaƙi da kwamandojin Boko Haram.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Shugaban Ƙasa Buhari ya ƙaddamar da sabuwar makarantar Chibok da aka sake ginawa kuma aka canza mata suna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban wanda ministan mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen ganin komai ya daidaita a garin Chibok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel