Tana Gama Rera Waka, Fitacciyar Jarumar Nollywood ta Yanke Jiki ta Fadi Matacciya

Tana Gama Rera Waka, Fitacciyar Jarumar Nollywood ta Yanke Jiki ta Fadi Matacciya

  • Fitacciyar mawakiya kuma jarumar Nollywood, Ms Onyeka Onwenu wadda aka haifa a ranar 31 ga watan Janairun 1952 ta rasu
  • An ce ta rasu ne a wani asibiti da ke Legas bayan ta yanke jiki ta fadi a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli
  • Fim din Onwenu na farko shi ne 'Nightmare', inda ta fito mace mara haihuwa wacce ta dauki rainon wani jaririn da aka jefar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Rahotannin da muka samu na nuni da cewa fitaciyyar marubuciya kuma mai rera waka kuma ‘yar wasan kwaikwayo, Ms Onyeka Onwenu ta rasu.

An rahoto cewa jarumar Nollywood din, Ms Onwenu ta rasu da yammacin ranar Talata a Asibitin Reddington da ke Legas jim kadan bayan rera waka.

Kara karanta wannan

MTN sun rufe maka layi? Ga wata hanya mai sauki ta bude layukan da aka rufe

Fitacciyar jaruma kuma mawakiya, Ms Onyeka Onwenu ta rasu
An sanar da mutuwar fitacciyar mawakiya kuma jarumar Nollywood, Ms Onyeka Onwenu. Hoto: @AdoraNwodo
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Ms Onwenu ta yanke jiki ta fadi ne bayan ta yi wasa (na rera waka) a wurin bikin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ms. Onwenu ta yi wasa ne a wajen bikin cika shekaru 80 na Misis Okoli, kwararriyar likitan hada magunguna, kuma wacce ta kafa kamfanin sarrafa magunguna na Emzor a Legas.

Jarumar Nollywood ta kwanta dama

Wani ganau da ke wurin bikin lokacin da mawakiyar ta yanke jiki ta fadi ya tabbatar wa jaridar TheNiche wannan labari mai ban tausayi.

“Abin bakin ciki ne matuka. Onyeka Onwenu ta yi wasa a bikin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli a yau (Talata, 30 ga Yuli, 2024), bayan gama wasan ta yanke jiki ta fadi.
"An kai ta Asibitin Reddington inda aka tabbatar da cewa ta koma ga mahaliccinta."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

- A cewar ganau din.

Kadan daga rayuwar Ms Onyeka

Ms Onyeka mawaƙiya ce, marubuciyar waƙa, 'yar wasan kwaikwayo, mai fafutukar kare hakkin ɗan adam da zamantakewa, 'yar jarida, 'yar siyasa, kuma tsohuwar alkalin wani shiri na X Factor.

Jaridun Najeriya sun yi mata lakabi da “Elegant Stallion”, ta kasance tsohuwar shugabar cibiyar fasaha da al’adu ta jihar Imo, inji rahoton The Punch.

Fitacciyar mawakiya kuma jarumar Nollywood, Ms Onyeka Onwenu wadda aka haifa a ranar 31 ga watan Janairun 1952 ta rike matsayin shugabar cibiyar ci gaban mata ta kasa a 2013.

Fim din Onwenu na farko shi ne 'Nightmare', mace mara haihuwa da ta dauki rainon wani jaririn da aka jefar da shi, wanda Zik Zulu Okafor ya ba da umarni.

Jarumi Olu Jacobs ya kwanta dama?

A wani labarin, mun ruwaito cewa rahotanni sun karade shafukan sada zumunta cewa fitaccen jarumin Nollywood, Olu Jacobs ya rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

Sai dai a wani sako da matarsa, wadda ita ma jarumar Nollywood din ce, Joke Silva ta ce mijinta na nan da ransa, labaran da ake yadawa na mutuwarsa ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.