Guinness: Mutumin Arewa Ya Shiga Gasar Daukar Lokaci Mafi Tsawo Ana Karatu a Duniya

Guinness: Mutumin Arewa Ya Shiga Gasar Daukar Lokaci Mafi Tsawo Ana Karatu a Duniya

  • A yau ake sa ran Mubakar Bello ya shiga gasar daukar lokaci mafi tsawo ana yin karatu a bayyane a fadin duniya
  • Malam MB kamar yadda aka san shi, marubuci ne, ‘dan gwargwamaya kuma mai sharhi a kan al’umuran yau da gobe
  • Idan mutumun Bauchin ya yi nasara, zai karya tarihin da Rysbai Isakov ya kafa a Guinness World Records

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Mubakar Bello ya dauki damarar shiga gasar Guinness wanda ‘yan Najeriya suka rika shiga a ‘yan shekarun nan.

Mubakar Bello wanda aka fi sani da Malam MB zai jarraba sa’arsa na daukar awanni ana karatu a Guinness World Records.

Guinness World Records
Mubakar Bello (Malam MB) ya shiga gasar Guinness World Records Hoto: Malam MB/guinnessworldrecords.com
Asali: Facebook

Malam MB zai shiga Guinness World Records?

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

Malam MB ya shaida haka a shafinsa na Facebook a yammacin Asabar, yake cewa ya ci burin daukar awanni 130 yana karatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu wanda yake rike da wannan kambu a wajen Guinness wani mutumin kasar Turkiyya ne mai suna Mista Rysbai Isakov.

Rysbai Isakov ya shafe awanni 124 yana karatu a bayyane a watan Satumban shekarar 2022.

Daga yau Lahadi 21 ga watan Yuli 2023, Malam Mubarak Bello zai fara karatu a bainar jama’a domin kafa tarihi a fadin duniya.

Guinness ta ba Malam MB dama

Legit Hausa ta yi magana da Malam M. B kafin ya shiga gasar, ya kuma shaida mata cewa Guinness ta yi na’am ya shiga gasar.

Zai shiga gasar ne a sabuwar unguwar Gida Dubu da ke kusa da makarantar Raudah Academy a titin Maiduguri da ke jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Malamin musulunci ya yi wa gwamnati da matasa bulaliya a huduba

Meyasa Malam MB shiga gasar Guinness?

Kamar yadda ya fada mana, yunkurin ba saboda shiga tarihi ba ne kurum, yana kokarin ganin ya taimakawa yaran da su ke Afrika.

Akwai miliyoyin kananan yara da ba su zuwa makarantar boko a nahiyar Afrika, matashin yana son ganin sun samu ilmin boko.

Idan ya yi nasarar samun dala miliyan 1, za iyi amfani da su wajen inganta ilmi a Afrika.

Karin albashin ma'aikata a Najeriya

Idan aka dawo maganar albashi, an ji labari Bola Tinubu ya amince mafi karancin albashi ya koma N70, 000, amma har yanzu akwai aiki.

A yadda farashin kaya su ke a yau, da wahala karin albashin da za a yi ya yi tasirin da ake tunani domin tiyar shinkafar waje ta kai N5000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng