Kwantai: Wani Bawan Allah Ya Ceto Aisha Mai Abinci Daga Tafka Asara a Bauchi

Kwantai: Wani Bawan Allah Ya Ceto Aisha Mai Abinci Daga Tafka Asara a Bauchi

  • Daga karshe, wani bawan Allah ya sayi abincin Hajiya Aisha wacce ta yi korafi kan yaudararta da ka yi ta dafa abinci mai yawa
  • Aisha ta nemi taimakon al'umma bayan wani ya ba ta kwangilar dafa abinci har na mutane 9,000 amma ba ta sake ganinsa ba
  • Hakan ya jawo mutane da dama suka tausaya mata inda suk a yi ta yada bidiyon domin samun wanda zai taimaka mata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Bayan korafin da wata mai siyar da abinci ta yi a jihar Bauchi, wani bawan Allah ya sayi abincin gaba daya.

Matar mai suna Hajiya Aisha ta roki al'umma su taimaka mata bayan wani ba ta kwangilar dafa abinci har na mutane 9,000.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya kunyata 'yan siyasa a zaman makokin tsohon gwamna

Wani bawan Allah ya sayi abincin Aisha bayan an yaudare ta
Bayan korafi a kafofin sadarwa, wani bawan Allah ya raba Aisha mai abinci da jidali. Hoto: Barde Kerarren Ajiya.
Asali: Facebook

Bauchi: Wani bawan Allah ya taimaki Aisha

Wani mai suna Kwamred Ameen Sulaiman shi ya wallafa faifan bidiyon a shafin Facebook inda ya tabbatar an saye abincin gaba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ameen ya ce wani bawan Allah ne ya sayi abincin gaba daya inda ya raba ga al'umma mabukata.

Sai dai bai bayyana sunan wanda ya taimaki baiwar Allan ba yayin da wasu ke rade-radin cewa gwamnatin jihar Bauchi ne ta sayi abincin.

Mutane sun soki Aisha kan rashin tsari

Mutane da dama sun nuna alhini kan abin da ya faru da matar inda wasu ke yi mata addu'a domin samun rabuwa da abincin.

Sai dai wasu sun caccake ta kan rashin yarjejeniya da kuma bata wani kaso na kudin kafin fara dafa abincin tun da kwangila ne.

Wani ya yaudari mai abinci a Bauchi

Kara karanta wannan

Bidiyo: Wata mata ta nemi taimakon ƴan Arewa, ta faɗi yadda wani mutumi ya cuce ta

Kun ji cewa wata mata ta bayyana yadda wani mutum ya buƙaci ta girka abincin mutane sama da 9,000 da za a raba kyauta ga mabuƙata a kananan hukumomi uku.

Awani faifan bidiyo, an ji Hajiya Aisha na bayanin yadda mutumin ya tuntuɓe ta kan girka abincin mutum 9,800, amma daga ƙarshe ya daina ɗaukar kiranta.

A cewarta, ta yi ƙoƙarin ganin mutumin ya ba ta takardar yarjejeniyar kwangilar dafa abincin amma ya roƙi ta ci gaba da aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel