Duk da Ikirarin Gidansa 1 Tak, an Gano El Rufai Ya Mallaki Gidan $193,084 a Dubai
- Wani bincike da masu shirin fallasa rashawa (OCCRP) tare da hadin guiwar jaridu 70 suka yi, ya nuna Nasiru El-Rufai ya mallaki gida a waje
- Kamar yadda binciken ya nuna, El-Rufai na daga cikin manyan 'yan siyasa, sojoji, alkalai akalla 200 da aka gano sun mallaki kadaroi a Dubai
- Abin mamaki, shekara daya kafin a fitar da wannan rahoton, tsohon gwamnan na Kaduna ya yi ikirarin cewa gida tak ya mallaka a rayuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A ranar Litinin ne rahoto ya fita na jerin wasu manyan 'yan siyasar Najeriya (PEPs), da jami'an tsaro da suka mallaki kadarori masu tsada a kasar Dubai.
Ba iya 'yan siyasa ko jami'an tsaro ba, akwai sunayen iyalan 'yan siyasar, alkalan kotu, manyan ma'aikatan gwamnati da suka kai 200 a jerin mamallakan kadarori a Dubai.
'Yan Najeriya masu gida a Dubai
Kamar yadda rahoton jaridar BusinessDay ya nuna, wannan fallasar na daga cikin binciken ƙwaƙwaf da tawagar 'yan jaridu ke yi kan kadarorin da 'yan Najeriya suka mallaka a Dubai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani rahoto da hukumar filaye ta Dubai ta fitar, ya nuna cewa 'yan Najeriya ne na biyu bayan kasar India da suka fi mallakar kadarori a kasar.
Atiku Abubakar, Nasiru El-Rufai, Lateef Olasunkanmi Fagbemi, Yusuf Datti Baba-Ahmed, Attahiru Bafarawa da sauran su, na a cikin wannan jerin sunayen.
Gidajen tsofaffin gwamnonin Kaduna a Dubai
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsofaffin gwamnonin Kaduna, Ahmed Makarfi da Nasiru El-Rufai na daga cikin wadanda rahoton ya ce sun mallaki gida a Dubai.
Yayin da aka ce Makarfi ya mallaki gida a Burj Khalifa mai darajar $822,016 (N1,258,416,074) an ce El-Rufai ya mallaki gidan da kudinsa ya kai $193,084 (N295,590,364) a Al Hebiah III.
Abin mamaki shi ne, shekara daya kafin a fitar da wannan rahoton, El-Rufai ya yi ikirarin cewa bai mallaki gida ko daya a wajen Kaduna ba, gidansa daya ne tak, kuma yana Kaduna.
"Gida na 1 rak a Kaduna" - El-Rufai
A wata tattaunawa da wani gidan rediyo, El-Rufai ya ce ko kadan bai taba daukar kudin jihar Kaduna ya kai su ketare ba.
Ya kuma ƙalubalanci wadanda suka gabace shi a shugabancin jihar, da su rantse da Allah cewa ba su saci kudin jihar Kaduna ba, kamar yadda rahoton PM News ya nuna.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce:
"Ina alfahari da titunan da na shimfida wadanda za su dade ana mora. Ba mu kwashi kudin jiha mun tafi Dubai mun saye gida ba, kuma ba mu je titin Jabi mun gina gida ba.
"Na zama gwamnan Kaduna ne ina da gida daya wanda ke kan titin Unguwan Sarki, Kaduna. Na kammala mulkina, Alhamdulillah, wannan gidan ne kaɗai na mallaka."
Abba ya ba Aminu Bayero sabon umarni
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ba Aminu Ado Bayero sabon umarni na ya gaggauta ficewa daga fadar Nasarawa.
Gwamnatin Kano ta ce abin takaici ne yadda har yanzu sarkin Kano na 15 ke ci gaba da zama a fadar duk da an ba shi umarni ya fita saboda za a yi gyara a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng