“Sirrin Hada Aikin Asibiti da Gidan Aure, Har Na Zama Farfesa”, Dakta Hadiza Galadanci

“Sirrin Hada Aikin Asibiti da Gidan Aure, Har Na Zama Farfesa”, Dakta Hadiza Galadanci

  • Hadiza Shehu Galadanci fitacciyar likita ce wanda tayi fice ba a Najeriya kadai ba, har a sauran kasashen duniya
  • Likitar ta yi karatu a jami’ar ABU Zariya daga nan ta tafi Legas har zuwa Ingila domin kwarewa a harkar lafiyar mata
  • Farfesa Hadiza Shehu Galadanci ta ba yara masu tasowa da kuma masu sha’awar zama irinta sirrin nasarar rayuwa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Hadiza Shehu Galadanci tayi fice a duniya a bangarenta na kiwon lafiya musamman sha’anin ilmin mata da harkar juna biyu.

Farfesa Hadiza Shehu Galadanci mace ce daga Arewa maso yammacin Najeriya wanda ta shiga mujallar Time cikin manyan gwarazan duniya.

Farfesa Hadiza Galadanci
Farfesa Hadiza Galadanci daga Kano tayi fice a duniya Hoto: buk.edu.ng
Asali: UGC

Hadiza Galadanci a 'Idan ka ji wane...'

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

A yammacin Juma’a aka samu yin hira da Hadiza Shehu Galadanci a shirin Idan ka ji wane ba banza wanda Dr. Adamu Tilde ya samu shiryawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwararriyar likitar ta bayyana irin gudumuwar da ta samu daga iyalinta da kuma mai gidanta wajen zama mashahuriyar likita kuma Farfesa.

Sirrorin nasarar Farfesa Hadiza Galadanci

A hirar da aka yi da ita a shafin Adamu Tilde, likitar ta bayyana sirrin cigabarta a rayuwa ganin yadda ta hada aikin asibiti da na gidanta.

Hadiza Galadanci ta ce lokacin abu, to ayi shi, saboda haka idan ta je asibiti sai ta maida hankalinta gaba daya wajen kula da marasa lafiya.

Bayan maida hankali ga aiki, ta ce ta samu ilmi sai uwa-uba, goyon baya daga iyayenta da mai gidanta wadanda sune tubali a rayuwa.

Da zarar ta dawo gida kuma sai ta ji da dawainiyar iyali abin da zai ba matan zamani mamaki. Wannan baiwar Allah ta haifi 'ya 'ya har hudu.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta ba 'yan mata masu shirin shiga fim shawara

Saboda rayuwar da ta dauka ne ta ce ba ta samun lokacin da za ta ziyarci wata kawa ko makamanciyar haka sai dai zumunci wajen biki.

Farfesa Galadanci: "Ayi hattara da zamani"

A yanzu duniya ta canza, wasu matan su kan dauko wani bakin salo wanda Farfesar ta ce ya zama dole al’umma suyi hattara da su a yau.

Likitar ta ce dole tun farko yara su samu tarbiyya daga gida domin idan babu tarbiyar, dole su fada tarkon zamani da ya lalata gidan aure.

Duk da tarbiya, Hadiza Galadanci wanda ta halarci jami’ar ABU a 1970s ta ce dole a samu abokan kwarai kuma iyaye su sake da yaransu.

Ta ce kyau yaro ya iya zama da iyayensa idan ba haka ba za su tafi dandalin sada zumunta wanda a nan ake yin barbarar miyagun dabi’u.

Kamar yada Legit Hausa ta samu labari, an kirkiro wannan shiri ne domin kara fito da gwarazan mutanen da suka yi fice daga yankin Arewa.

Kara karanta wannan

'Aikin banza ake yi' Naziru Sarkin Waka ya ragargaji 'yan kirifto masu jiran ta fashe

A baya an yi hira da irinsu Usman Isiyaku, Bala Mohammed, Ibrahim Dooba, Aliyu Tanko, Abubakar Gambo, Aliyu Dahiru da Abba Hikima.

Alheran Gbemisola Ruqayyat Saraki

A watan jiya aka samu labari cewa tsohuwar karamar ministar sufuri, Gbemisola Ruqayyat Saraki ta cika shekara 59 da haihuwa.

A jiya wasu suka fara jin ayyukan alheran da ‘yar siyasar tayi wa musulman da ke kusa da ita, Sanata ta kai mutane da yawa aikin hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel