Zainab Ado Bayero: Labarin 'Yar Sarkin Kano da ta Bambanta da Jikokin Gidan Dabo

Zainab Ado Bayero: Labarin 'Yar Sarkin Kano da ta Bambanta da Jikokin Gidan Dabo

Abuja - Zainab Ado Bayero jinin sarautar Kano ce, cikakkiyar ‘yar gidan dabo, ta na cikin ‘ya ‘yan Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kwanan nan Zainab Jummai Ado Bayero ta rika shiga labarai sosai musamman saboda tarihin mahaifinta da ta ke kokarin fito da shi.

Zainab Ado Bayero
Zainab Ado Bayero tana aiki a kan tarihin Marigayi Sarkin Kano Hoto: blueprint.ng/www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Legit Hausa tayi kokari wajen tattaro maku bayanai game da Zainab Ado Bayero:

Wacece mahaifiyar Zainab Ado Bayero?

Hajia Hauwa Momoh ita ta haifi Zainab Ado Bayero, ita kuwa asalinta diya ce wajen Sarkin Auchi a Etsako da ke Arewacin jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ta ce Mai martaba Ahmed Momoh ya kai diyarsa karatu a jami’ar Bayero da ke Kano a 1984, ya damka ta ga Alhaji Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Tafiyar karshe da Aminu Ado Bayero yayi da bai sake shiga fadar Sarkin Kano ba

Ado Bayero ya haifi Zainab Jummai?

Hauwa Guruza Momoh ce haifawa Sarki Ado Bayero yara biyu, Zainab da Ahmad Tijjani sai dai a halin yanzu ba su zama a Kano.

Jummai watau Zainab tana cikin wadanda Sarkin Kano na 13 ya haifa a karshe.

Korafin 'yan dakin Zainab Ado Bayero

A wata hira da aka yi da su a jaridar Fronline, sun ba da labarin yadda suka rasa matsuguni bayan Sarki ya rasu a Yunin 2014.

'Yan dakin Momoh sun yi ikirarin ba a ba su hakkokinsu ba bayan rasuwar basaraken wanda ya shafe shekaru yana mulkin Kano.

A cewarsu da farko Mai martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya zama Sarkin Bichi daga baya ya rika dawainiya da ‘yanuwansa.

Zainab: ‘Yar Sarkin Kano ta fita zakkah?

Zainab tana cikin ‘yan autan ‘ya ‘yan Ado Bayero ta sha bam-bam da akasarin mutanen Arewa, saboda haka ta jan hankali jama’a.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

Kamar yadda ta taba fadawa Premium Times, ba kowane lokaci ta ke yin lullubi kamar yadda aka saba a garuruwa kamar Kano ba.

A Arewa ba a san yara da bijirewa manya ba, wannan yana cikin inda Zainab ta kan sam matsala, ta kan kalubalanci wannan al’ada.

Wasu suna yiwa mata kallon banzai dan ba su yin shiga ta lullbi, diyar Sarkin ta ce duk da tana da tarbiya, ta kan yi yawo babu hijabi.

“Na san fadin hakan abin kunya ne, amma na kan so in fita dabam. Ni musulma ce da ta yarda da musulunci da shika-shikai biyar na addinin.”

Inda Zainab ta biyo Ado Bayero

Amma kuma a cewarta ta biyo mahaifinta wajen gudun jama’a da son lemun soda da 7-up sannan ita ma tana da son yawan karatu.

Idan ba domin sarauta ba, Zainab ta ce mahaifinsu ba zai zama mai shiga jama'a ba.

Kara karanta wannan

Diyar Ado Bayero ta turawa Tinubu da Abba sako, tayi zancen rigimar masarautar Kano

Wasu kuma suna cewa ba a raba hanta da jini, idan mutum ya lura da kyau, zai fahimci Zainab tana kama da 'ya 'yan Ado Bayero.

Zainab tana aikin tarihin Ado Bayero

Yanzu dai Zainab na kokarin wallafa tarihin mahaifinsu kuma ta ce ta gagara samun gudumuwa daga gwamnatoci da manyan Arewa.

Wadannan kalubale ba su taka mata burki ba, ta dage sai ta fito da tarihin Ado Bayero.

Sakon Zainab Ado Bayero ga Bola Tinubu

A baya an rahoto diyar marigayi sarki Ado Bayero tana tunatar da shugaba Bola Tinubu ya gaggauta duba halin da ‘yan kasa ke ciki.

Zainab Ado Bayero ta yi tunatarwar ne inda ta ce akwai talauci da rashin kaunar juna a zuciyoyin ‘yan Najeriya wanda ya kamata a gyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel