Bamu da gidan zama, an hana mu komai na gado - Daya daga matan marigayi Ado Bayero
- Daya daga cikin iyalan marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ta magantu
- Hajiya Hauwa, wacce ta haifa masa 'yaya biyu ta bayyana irin halin kuncin da suke ciki
- Tana kira ga gwamnati ta kawo musu dauki saboda ko gidan zama basu da shi
Hajiya Hauwa Momoh, daya daga cikin matan marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da diyarta, Zainab Ado Bayero, sun bayyana yadda suka zama abin tausayi bayan manyan 'yayan mahaifinsu sun manta da su.
Hajiya Hauwa ta zauna da jaridar Saturday Sun inda ta bayyana halin da ita da yaranta biyu; Zainab da Ahmed Tijjani da ta haifawa Ado Bayero suka shiga.
Hajiya Hauwa, wacce diya ce ga tsohon Otaru na Auchi a jihar Edo, ta bayyana cewa mijinta da manyan yaransa suna kula da su sosai kafin rasuwar Sarki Ado a 2014.
Amma tun bayan rasuwarsa aka koresu daga gidan da suke zaune a Kano, kuma yanzu basu da wani gidan zama kuma babu abinda aka basu na gidajensa.
Zainab ya ce babban dan marigayin ya yi musu alkawari sau tari amma ba ya cikawa. Ta ce ana cin mutuncinsu saboda mahaifiyarsu ba 'yar arewa bace.
KU KARANTA: Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a
DUBA NAN: Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro
Hajiya Hauwa tace: "Kun san a Kano, idan kai ba dan can bane, haka suke yi. Lokacin da Bayero ya rasu, sun yi alkawarin taimaka mana amma kowani shekara sai na rokesu. Su kan ce mana zasu taimaka amma shekaru shida yanzu babu."
"Shekaru shida yanzu da rasuwarsa, babu wanda ya neme mu. Diyata tana son muyi magana amma duk lokacin da mukayi magana, ba zasu amsa ba."
Diyarta, Zainab Bayero tace: "Nasiru Ado Bayero, wanda shine Sarkin Bichi da Aminu Ado Bayero wanda shine sarkin Kano yanzu sun yi alkawari bayan rasuwa babanmu amma har yanzu. Ban san dalilin da yasa suka sharemu ba."
Ta ce tun lokacin da ta kammala karatun sakandare, ta gaza cigaba yayinda kaninta, Ahmed Tijjani, har yanzu bai cigaba daga aji 4 a sakandare ba.
Saboda haka tana kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka mata da kaninta saboda su koma makaranta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng