‘Alex ya dawo Abdulaziz’: ‘Dan Majalisar Abia Ya Zama Musulmi, Ya Karbi Kalmar Shahada

‘Alex ya dawo Abdulaziz’: ‘Dan Majalisar Abia Ya Zama Musulmi, Ya Karbi Kalmar Shahada

  • Alex Ifeanyi Mascot Ikwechegh ya bar addininsa, ya zama musulmi kamar yadda wani ya yada a dandalin sada zumuntan zamani
  • Mansur Ringim ya ce sun idar da sallah kenan a masallaci, sai ga ‘dan majalisar yana kokarin karbar shahada a birnin Abuja
  • Mutane musamman musulmai sun yi farin ciki ganin yadda ‘dan majalisar wakilan tarayyar mai-ci ya rungumi addininsu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Alex Ifeanyi Mascot Ikwechegh ya zama musulmi a sakamakon karbar kalmar shahadar addinin musulunci da ya yi.

Hon. Alex Ifeanyi Mascot Ikwechegh ‘dan siyasa ne wanda yanzu haka yake wakiltar Aba ta Arewa a majalisar wakilan tarayyar.

Hon. Alex Ikwechegh Mascot
Hon. Alex Ikwechegh Mascot ya zama musulmi a Abuja Hoto: @MSRingim
Asali: Twitter

Mansur Ringim ya sanar da haka a shafinsa na X wanda ya fi shahara da Twitter.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi hasashen dawowar Sanusi II kuma ta tabbata bayan kwanaki 1538

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar Abia ya zama musulmi

A cewar Malam Mansur Ringim, sun kammala wata sallar azahar kenan sai ga ‘dan majalisar wakilan ya zo zai musulunta.

Hon. Alex Ikwechegh Mascot ya karbi kalmar shahada ne a masallacin Salam da ke unguwar Maitama a birnin tarayya Abuja.

Bayan shigowarsa musulunci, Ringim ya ce yanzu wannan mutumi da aka fi sani da Alex Ikwechegh Mascot, ya canza sunansa.

Tuni ya koma Abdulazeez kamar yadda aka san mutane su kan canza sunayensu idan sun shigo musulunci daga wani addini.

"Alhamdulillah…Bayan mun gama sallar zuhur a masjid salam Maitama, sai ga Danmajalisar Tarayya mai ci daga Abia Hon. Alex Ikwechegh Mascot ya karbi Sha’hada.
Allaahu Akbar. Yanzu sunan sa Abdülaziz Allaah ya karfafi musulunci, ya sa sanadiyyar sa wasu ma şu musulunta, Aameen."

Hakan yana zuwa ne watanni bayan ‘dan majalisar ya yi ta shari’ar takara, ya kalubalanci nasarar LP a 2023, kuma ya dace.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Ba ga siyasa, Alex Ikwechegh babban ‘dan kasuwa ne wanda ya shiga harkar gine-gine da saida mai kuma ya na da gidauniya.

Haifaffen na Igbere a karamar hukumar Bende ya taba zama shugaban karamar hukuma a Abia ya na mai shekara 28 a duniya.

Musulmai na kukan rashin gata a yankinsa, suna cewa an maida su saniyar ware.

Alakar Najeriya da kasar UAE

A baya, rahoto ya ce Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nuna babu abin da zai sa tayi rigima da kamfanin jiragen Emirates da ke UAE.

Wani jagora a PDP, Osita Chidoka ya yi kaca-kaca da kamfanin, ya zarge shi da juyawa Najeriya baya, ya ce kyau a yi watsi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng