'Dan Najeriya Zai Shafe Sa’o’i 24 a Cikin Kabari, Zai Yada Bidiyon Gasar Kai Tsaye
- Wani matashi dan Najeriya ya yi yunkurin kafa sabon tarihi yayin da za a binne shi da ransa a cikin akwatin gawa na tsawon sa'o'i 24
- A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, Young C ya bayyana dalilin shiga wannan gasar yayin da ya yi alkawarin yada bidiyo kai tsaye
- Rahotanni sun nuna cewa wani dan kasar Amurka da ya yi suna a YouTube, MrBeast (Jimmy Donaldson) ya shiga irin wannan gasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wani dan Najeriya mai suna Young C ya shiga cikin wata irin gasa ta a saka mutum a akwatin gawa sannan a binne shi da ransa na tsawon sa'o'i 24.
Za a binne Young C da rai a kabati
Jaridar Vanguard ta ruwaito Young C a shafinsa na Instagram a ranar Laraba ya bayyana cewa zai yi komai a idon jama'a domin gudun ace ya yi coge.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana aniyarsa ta watsa faifan bidiyo kai tsaye daga akwatin gawar da za a saka shi har zuwa binne shi a kabarin da kuma zama a ciki na awanni 24.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda wani mai amfani da X ya wallafa a ranar Laraba, 8 ga Mayu, Young C ya ce:
"Zan shafe sa'o'i 24 a cikin wannan akwatin gawar, mutane na ku sani wannan lamarin gaskiya ne ba karya ba.
"Kuma abin da zai fi ba ku sha'awa shi ne, zuwa dare zan fara yada maku bidiyon abin da ke faruwa kai tsaye."
An taba binne Young C
A cikin bayanin da ya bayar daga baya, Young C ya bayyana cewa an taba binne shi na sama da sa'o'i 8 kuma ya fuskanci sauyin yanayi a jikinsa gami da yawan zufa da ya yi.
A bayanin da ya fitar a yammacin Laraba, ya ce:
“Mutane na, an binne ni da raina na sama da sa'o'i 8 yanzu. Ga wadanda kuka kalli bidiyona na farko, to har yanzu dai ina a nan.
Kamar yadda kuke gani, kyamarata har yanzu tana aiki, kuma ina da sauran haske a nan, amma fa sai faman gumi nake yi."
Kalli bidiyon a kasa:
Hanyoyin kawar da tsaka daga gida
A wani rahoton, Legit Hausa ta kawo wasu dabaru guda shida da mutane za su iya amfani da su domin hana tsaka ta zauna a gidajensu.
A 'yan kwanakin nan, ana ta samun rahotanni na irin barnar da tsaka ke yi musamman wajen saka guba a abincin mutane da kuma jawo gobara.
Asali: Legit.ng