Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki

Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki

- A yau Asabar 14 ga watan Nuwamba ne za a birne fitaccen attajirin ɗan kasuwan Zimbabwe, Ginimbi

- Za a birne Ginimbi a katafaren gidansa da ke Domnoshava a akwatin gawar ƙirar Versace

- An yi ƙiyasin cewa kudin akwatin gawar ya kai Dalar Amurka 5000 zuwa 12000

Za a birne fitaccen ɗan kasuwar kasar Zimbabwe, Genius Ginimbi Kadungure a yau 14 ga watan Nuwamban 2020 cikin akwatin gawa ƙirar Versace kamar yadda LIB ta ruwaito.

Ginimbi ya rasu ne a ranar 8 ga watan Nuwamba a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa biki zagayowar ranar haihuwar wata ƙawarsa.

Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki
Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki
Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

Idan za ka iya tunawa an ruwaito cewa marigayin ya siya akwatin gawa mako guda kafin rasuwarsa a hatsarin da ya yi sanadin mutuwar fitacciyar mai fitowa a bidiyo Mitchelle Amuli da aka fi sani da Moana.

KU KARANTA: Mutane 18 sun rasu a hadarin kwale-kwale a Bauchi

Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki
Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki
Hotunan akwatin gawa ƙirar 'Versace' da za a birne attajiri Ginimbi ciki. Hoto: @lindaikeji
Asali: Instagram

A cewar kafafen watsa labarai na ƙasar Zimbabwe, ƴan uwansa sun ce ba gaskiya bane ya siyo akwatin gawa.

Sun bayyana cewa za a birne shi a akwatin gawa ƙirar Versace a katafaren gidansa da ke Domnoshava a yau Asabar.

An ce ƙiyasin kuɗin akwatin gasar ta Versace ya kai $5000 zuwa $12000 kwatankwancin N4,565,997.10

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.

"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel