Pelumi Nubi: An Shiga Farin Ciki Yayin Da ’Yar Tattaki Daga Landan Zuwa Nijeriya Ta Isa Legas
- Kwanaki 68 matashiyar nan Pelumi Nubi ta kwashe tana tuki a mota daga birnin Landan zuwa jihar Legas ta Nijeriya
- An ruwaito cewa Nubi ta fara wannan tattakin ne a watan Maris kuma ta gamu da kalubale masu yawa ciki har da hatsarin mota
- Gwamnatin Legas ta tarbi Nubi a kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Benin, tare da yi mata maraba da sauka bayan wannan doguwar tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - Wata matashiya mai shekaru 28 mai suna Pelumi Nubi, wacce ta fara tattaki amma a mota daga Landan ta iso Legas.
Nubi ta fara tuki a motarta ne a ranar 31 ga watan Janairu kuma ta fuskanci cikas iri-iri a kan hanyarta, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Kwamishiniyar yawon shakatawa, Mrs Toke Benson-Awoyinka ne ta tarbe ta a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin a madadin gwamnatin jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Maris, Nubi ta tsallake rijiya ta baya-bayan a wani hatsarin mota da ya rutsa da ita, wanda ya lalata mata gaban mota da fasa mata gilashin gaba.
Jerin kasashen da Nubi ta ketare
Daga Ingila Nubi ta fara wannan tattaki, ta bi ta kasar Faransa, Sifaniya ta bulla Moroko, sannan ta bi ta saharar Yamma.
Daga nan ta bi ta Mauritaniya, Senegal, The Gambia, Guinea-Bissau, Guinea, Sierra Leone, Liberia, Mali, Burkina Faso, Côte d'Ivoire, Gana, Togo, Benin sannan ta shigo Legas.
Matashiyar a shekarar 2022 ta sanar da cewa ta ziyarci kasashe 77 a yayin da ta kai shekaru 22 a duniya, kuma ta cimma kasashe 80 cikin 193 da muke da su a duniya.
A nata mahangar, Nubi tana so ta shaidawa duniya cewa kalmar "ba zai yiwu ba" kawai ana fada ne idan ba a jaraba yi ba.
Gwamnatin Legas ta tarbi Nubi
Gboyega Akosike, mai ba gwamnan Legas shawara kan harkokin watsa labarai a ranar Lahadi ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
"Jihar Legas na maraba da wannan gwarzuwa @peluminubi_, 'yar Nijeriya mazauniya Birtaniya, wacce ta yi tattaki daga Landan zuwa Legas.
"Kwamishiniyar yawon bude ido, Mrs Toke Benson-Awoyinka da mai ba gwamna shawara kan yawon bude ido, @IdrisConnecting ne suka tarbe ta a iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Benin."
Kalli bidiyon da aka ɗauka lokacin da aka tarbi Nubi a Legas:
Nubi ta fara tuki daga Landan zuwa Legas
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Pelumi Nubi, jajurtacciyar 'yan Nijeriya ta sha alwashin yin tuki daga Landan zuwa Legas.
Motar Nubi an kerata ne musamman domin yin doguwar tafiya, kuma ta bayyana cewa akwai gado da ababen more rayuwa a cikin motar.
Asali: Legit.ng