Elon Musk ya tafka asarar N397.62bn a rana 1, ya fado daga na 2 a arzikin duniya

Elon Musk ya tafka asarar N397.62bn a rana 1, ya fado daga na 2 a arzikin duniya

  • Elon Musk a yanzu ba shi ne mutum na 2 da yafi kudi a duniya ba tunda ya rikito daga matsayin kamar yadda Forbes da Bloomberg suka ce
  • Wanda ya kirkiro Tesla ya rasa N397.62 biliyan a cikin sa'o'i 24, lamarin da yasa ya sauka daga matsayinsa a jerin masu arziki
  • Darajar kamfaninsa ta ragargaje yayin wannan asarar da ya tafka saboda masu zuba hannayen jari sun taya Tesla kasa da yadda yake a jiya

Arzikin wanda ya kirkiro Tesla, Elon Musk ya samu matukar girgiza inda ya sauka daga matsayinsa a jerin masu arzikin duniya.

A baya Musk ya kasance a mataki na biyu a jerin masu kudin duniya kamar yadda jerin biloniyoyin Forbes da Bloomberg suka bayyana.

KU KARANTA: Gwamnan Neja yayi fallasa, ya bayyana yadda 'yan bindiga ke hada kai da jami'an gwamnati

Elon Musk ya tafka asarar N397.62bn a rana 1, ya rikito daga zama mai arzikin duniya
Elon Musk ya tafka asarar N397.62bn a rana 1, ya rikito daga zama mai arzikin duniya. Hoto daga Pascal Le Segretain
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Da duminsa: EFCC ta gurfanar da jami'an gwamnatin Sokoto 5 kan damfarar

N500m

Kamar yadda Real Time Newt Worth na Forbes suka wallafa, mai SpaceX ya rasa N397.62 biliyan a ranar Talata bayan raguwa da dukiyarsa tayi da kashi 0.64%.

Wannan lamarin yasa ya rasa $150.1 biliyan kuma ya fada kasan Bernard Arnault da Jeff Bezos wadanda ke da $199.2 biliyan da $196.5 biliyan.

Tesla ya rage daraja

Arzikin Musk ya fadi bayan Tesla ya rage daraja, hakan yasa ya rasa N397.62 biliyan a cikin sa'o'i kamar yadda jerin biliniyoyi na Forbes ya bayyana.

Arzikinsa a jerin biloniyoyin na Bloomberg ya tsaya a $166 biliyan inda ya fada bayan Jeff Bezos da Bernard Arnault.

A wani labari na daban, tashin hankali da rashin natsuwa ya sauka a Ebenator dake Awo Omama a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo bayan 'yan bindiga sun kai farmaki garinsu dan majalisa mai wakiltar mazabar Orsu a majalisar jihar Imo, Ekene Nnodumele a ranar Laraba.

An gano cewa 'yan bindigan sun cire kan maigadi dake aiki kafin su bankawa gidan wuta, Daily Trust ta ruwaito.

Manema labarai sun tattaro cewa 'yan bindigan sun kone gidan tsohon antoni janar da kwamishinan shari'a, Cyprain Charles Akaolisa a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng