Jadawalin 2024: An Fitar da Jerin Jami’o’i 10 Mafi Inganci a Afirka

Jadawalin 2024: An Fitar da Jerin Jami’o’i 10 Mafi Inganci a Afirka

Shafin Edu Rank ya wallafa jadawalin 2024 na jami'o'in Afrika mafi inganci, wanda a bana ya fitar da jarin jami'o'i 100 a jadawalin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

EduRank ya fitar da jadawalin manyan jami'o'i 100 a Afirka ne bisa ga 'bayanan bincike' na kowacce jami'a, shaharar jami'a a fannin da ba na ilimi ba da kuma tasirin tsofaffin ɗalibai.

Jerin jami'o'in Afrika da suka fi shahara a 2024
Afrika ta Kudu ta fi kowacce kasa a Afrika yawan jami'o'i da suka shahara a duniya. Hoto: Kevin Dodge
Asali: Getty Images

Jami'ar Cape Town ce mafi girma

An kuma kimanta jami'o'in ne ta hanyar nazarin makalu 24.5m da aka samu daga wallafar ilimi 2.16m da jami'o'i 1,104 daga Afirka suka fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, an yi amfani da shaharar tsofaffin ɗalibai 3,700 daga jami'o'in, da kuma mafi girman bayanan makarantun da ake da su.

Kara karanta wannan

Yadda yajin aikin SSANU/NASU ya jawo silar mutuwar wani dalibin jami'a

A cewar Edu Rank, Jami'ar Cape Town (UCT) da ke a Afirka ta Kudu, wacce aka sanya a matsayi ta 242 a jerin jami'o'in duniya ita ce ta 1 a Afirka ta Kudu kuma ta 1 a Afirka.

Ga jerin jami'o'i 20 mafi inganci a Afrika

  1. Jami'ar Cape Town
  2. Jami'ar Wiwaterrand
  3. Jami'ar Stellenbosch
  4. Jami'ar Pretoria
  5. Jami'ar Cairo
  6. Jami'ar KwaZulu-Natal
  7. Jami'ar Makerere
  8. Jami'ar Nairobi
  9. Jami'ar Johannesburg
  10. Jami'ar Afirka ta Kudu
  11. Jami'ar Ghana
  12. Jami'ar North-West
  13. Jami'ar Ibadan
  14. Jami'ar Rhodes
  15. Jami'ar Alexandria
  16. Jami'ar Ain Shams
  17. Jami'ar Western Cape
  18. Jami'ar The Free State
  19. Jami'ar Addis Ababa
  20. Jami'ar Amurka dake Cairo

Jadawalin 2024: Cikakken jawabin jami'o'i 10

A ƙasa akwai cikakken jerin da taƙaitaccen bayanai na manyan jami'o'i 10 mafi kyau a Afirka a 2024 (bisa ga matsayin Edu Rank 2024):

1. Jami'ar Cape Town

Jami'ar Cape Town (UCT) jami'ar bincike ce ta jama'a da ke garin Cape Town, Afirka ta Kudu.An kafa ta a cikin 1829 a matsayin Kwalejin Afirka ta Kudu, amma an ba ta cikakken matsayin jami'a a 1918.

Kara karanta wannan

Mutuwa rigar kowa: Fitaccen Furodusan fina-finai a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Hakanan ita ce jami'a mafi tsufa a yankin Saharar Afirka da har yanzu ake karatu a cikinta.

2. Jami'ar Wiwaterrand

Jami'ar Witwatersrand, Johannesburg, jami'ar bincike ce ta jama'a da yawa wacce ke a arewacin tsakiyar Johannesburg, Afirka ta Kudu.

An kafa ta a cikin 1896 a matsayin makarantar ma'adinai ta Afirka ta Kudu a Kimberley, ita ce jami'a ta uku mafi tsufa a Afirka ta Kudu da har yanzu take aiki.

3. Jami'ar Stellenbosch

Jami'ar Stellenbosch babbar cibiyar koyarwa ce ta Afirka.

Jami'ar ta ce an kafa ta ne domin ta zamo babbar jami'a mai zurfin bincike a Afirka, wacce aka amince da ita a matsayin mafi kyawu, inganci da sabbin kayan koyarwa.

4. Jami'ar Pretoria

Jami'ar Pretoria (UP) tana ɗaya daga cikin manyan jami'o'in Afirka kuma babbar jami'ar hulɗa da jama'a a Afirka ta Kudu.

Tana alfahari da kanta a matsayin "babbar jami'a mai zurfin bincike a Afirka, wadda aka sani a duniya don ingantaccen iliminmu, da tasirin dalibanmu".

Kara karanta wannan

Zai yi wahala APC ta kai labari, jiga-jigan jam'iyya sun gargadi Tinubu kan halayen Minitansa

5. Jami'ar Cairo

Jami'ar Cairo jami'a ce ta bincike mai daraja ta duniya wadda ta wallafa makalun ilimin kimiyya 83,519, kuma ta karɓi makalu 948,187.

Jami'ar wadda aka kafa a ranar 21 ga Disamba 1908; an fara saninta da sunan jami'ar Masar daga 1908 zuwa 1940, daga baya ta koma jami'ar Sarki Fuad I da kuma jami'ar Fu'ād al-Awwal daga 1940 zuwa 1952.

6. Jami'ar KwaZulu-Natal

Jami'ar KwaZulu-Natal jami'a ce mai cibiyoyin karatu biyar a lardin KwaZulu-Natal da ke a Afirka ta Kudu. An kafa ta a ranar 1 ga Janairu 2004 bayan haɗewar jami'ar Natal da jami'ar Durban-Westville.

Ita ce jami'a mafi girma a Afrika ta Kudu, kuma ta 613 a jarin jami'o'in duniya. UKZN ta yi suna sosai a fannonin kimiyya, fasaha, injiniyanci, da lissafi.

7. Jami'ar Makerere

Jami'ar Makerere ita ce babbar jami'ar ilimi mafi girma a Uganda, wacce aka fara kafa ta a matsayin makarantar fasaha a 1922, kuma jami'a mafi tsufa a halin yanzu a Gabashin Afirka.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dinke ɓarakar da ta kunno kai a APC, an sauya mataimakin dan takarar gwamna

Jami'ar Makerere ya yaye manyan shugabannin Afirka, ciki har da shugaban Uganda Milton Obote da shugabannin Tanzaniya Julius Nyerere da Benjamin Mkapa da sauran su.

8. Jami'ar Nairobi

Jami'ar Nairobi (uonbi ko UoN) jami'ar bincike ce ta haɗin gwiwa da ke Nairobi kuma ita ce babbar jami'ar a Kenya.

Kodayake tarihinta a matsayin cibiyar ilimi ya kasance tun 1956, sai dai ba ta zama jami'a mai zaman kanta ba sai a 1970.

9. Jami'ar Johannesburg

Jami'ar Johannesburg (UJ) ta na a lardin Johannesburg Gauteng da ke Afirka ta Kudu. Ana karatun digiri na farko da na biyu a jami'ar, kuma dalibai na iya yin karatu a yanar gizo.

An kafa jami'ar Johannesburg ne a ranar 1 ga Janairu 2005 sakamakon haɗewar jami'o'in Rand Afrikaans (RAU), Technikon Witwatersrand (TWR) da cibiyoyin Soweto da Gabashin Rand na Jami'ar Vista.

10. Jami'ar Afirka ta Kudu

Jami'ar Afirka ta Kudu (UNISA) ita ce babbar jami'a a Afirka ta Kudu ta hanyar yawan masu shiga. Ita ce ke da kaso uku na dukkan daliban da ka karatu a jami'o'in ta Kudu.

Kara karanta wannan

"Har yanzu ni mamban jam'iyyar PDP ne" Ministan Tinubu ya yi magana kan sauya sheƙa zuwa APC

Tun bayan kafa ta a cikin 1873 a matsayin jami'ar Cape of Good Hope, jami'ar Afirka ta Kudu (ko Unisa kamar yadda aka fi saninta) ta kasance a matsayin cibiyar bincike ta jami'o'in Oxford da Cambridge.

Jami'o'i 10 mafi girma a Najeriya

A wani rahoton makamancin wannan, Legit Hausa ta tattaro bayani kan jerin jami'o'i 10 da suka fi girma a Najeriya, musamman ta fuskar yawan kadada, kyawun gini da tsarin koyarwa.

Duk da dai girma jami'a ba wai shine abinda zai saka dalibi ya zabe ta ba a matsayin inda zai yi karatu, amma dai wannan labari yana da matukar amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.