"Ya Kashe Sama da N30m": Magidanci Ya Shiga Damuwa da Matarsa da Ya Kai Turai Ta Nuna Halinta

"Ya Kashe Sama da N30m": Magidanci Ya Shiga Damuwa da Matarsa da Ya Kai Turai Ta Nuna Halinta

  • Wani magidanci da ya koma Birtaniya tare da matarsa ​​a yanzu ya yi nadamar hakan saboda matar tana cin amanarsa
  • An ce mutumin ya kashe sama da Naira miliyan 30 wajen tabbatar da bizarsu, amma matar hankalinta ya koma wajen tsohon saurayinta
  • Matar ta ziyarci tsohon saurayinta wanda ke zaune a Plymouth, inda ta kashe fam 100 a jirgin ƙasa daga Dundee domin ta ci amanar mijinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata mata ƴar Najeriya ta ci amanar mijinta, wanda ya ɗauke ta zuwa ƙasar Burtaniya

Labarin ma'auratan da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna cewa matar ta kwanta da tsohon saurayinta.

Matar aure ta ci amanar mijinta
Magidanci ya yi da-na-sanin kai matarsa Birtaniya Hoto: Getty Images/Rick Gomez and Vladimir Vladimirov. Hotunan an yi amfani da su ne kawai don misali
Asali: UGC

A cewar labarin da @Iampenlord ya sanya a shafinsa na X, magidancin da matarsa ​​sun samu takardar bizar ma'aurata kuma suka koma Burtaniya a matsayin ƙwararrun ma'aikata.

Kara karanta wannan

Zaman majalisa ya samu cikas yayin da aka shiga duhu, bidiyo ya bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya kasance wanda ya ɗauki nauyin bizar kuma ya kashe kuɗi har Naira miliyan 30.

Lokacin da suka isa Birtaniya, matar ta nemi tsohon saurayinta, wanda ke zaune a Plymouth, kuma ta je wajensa don su sheƙe ayarsu.

Wani ɓangare na labarin na cewa:

"Kwanaki da suka wuce, matar ta yi tafiyar sa’o’i 10 daga Dundee (a Scotland) zuwa Plymouth (a Ingila) domin ta je ta yi lalata da tsohon saurayinta."
"Tsohon saurayin shi ne wanda ya riƙa haifar da faɗace-faɗace a tsakaninsu tun lokacin da suke a Najeriya."
"Mijin ya so ta yanke hulɗa da tsohon saurayin na ta, amma uzurinta ya kasance, 'mu tsaffin masoya ne kawai ba maƙiya ba'."

Magidancin dai yana cikin matsala domin ba zai iya ɗaukar wani mataki a kan matarsa ba, wacce da sunanta aka nemi bizarsu, domin gudun kada a dawo da shi Najeriya.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: An samu hanyar da za a kawo karshen 'yan bindiga a Najeriya

Wane martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Jonneto2 ya rubuta:

"Ba dole sai ya tilasta kansa ya tsaya a cikin auren ba idan har ba ya so. Don ya sake ta ba shi ke nufin za a dawo da shi Najeriya ba, kawai ya tattara hujjojinsa. Shi namiji ne zai iya rayuwa a karon kansa."

@TunjiStillDey ya rubuta:

"Alamun matsala sun bayyana ƙiri-ƙiri tun kafin su bar gida. Ta yaya bai lura da hakan ba? Bana son na sani. Da zarar wanda kuke tare yana tare da hulɗa da tsohon wanda suka yi soyayya a baya, dole a samu matsala a ƙarshe."

@Iampenlord ya rubuta:

"Bayar da shawara da yin suka suna yi mana daɗi a baki da zarar ba mu ba ne abin ya faru a kanmu ba."

Ƴar Najeriya da ke karatu a UK na neman taimako

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƴar Najeriya da ke karatun digiri na biyu a UK ta koma neman taimakon jama'a.

Omolola Bowoto ta bayyana cewa tana shekara ta biyu a jami'ar Sussex kuma da wata biyar kaɗai ya rage mata ta kammala karatun, amma za a koro ta saboda gaza biyan kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng