Dangote Ya Barke da Kuka a Wajen Makokin Wigwe, Ya Fadi Abu 1 da Zai Yi Domin Tuna Marigayin
- Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote ya barke da kuka saboda rasuwar Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings
- Dangote ya kuma sanar da sauya sunan babbar hanyar matatar mansa zuwa sunan Wigwe, wanda ya kira shi da sunan 'ginshiki' a rayuwarsa
- Wigwe ya mutu ne tare da matarsa da dansa, da kuma tsohon shugaban kungiyar canjin kudi ta Najeriya, a wani hatsarin jirgin sama a Amurka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ikoyi, Legas - An hasko Aliko Dangote yayin da ya barke da kuka a lokacin da yake ta'aziyyar marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Wigwe ya mutu ne tare da matarsa da dansa, Chizoba da Chizi, a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka.
Dangote ya yi ta'aziyyar Herbert Wigwe
Yayin da yake saka hannu a rajistar ta'aziyyar marigayin wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, Dangote ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Duk da cewa, tsohon hamshakin ma'aikacin bankin bai shiga aikin soja ba; amma ina kallonsa a matsayin soja mazan fama."
A cewar Dangote, mutane sun nuna wa Wigwe soyayya ta gaskiya kuma ya yi rayuwar da ta dace a yi koyi da ita.
Dangote ya yi wani abu na tunawa da Herbert Wigwe
A yayin da ya ke mika ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kamfanin Access Bank Holdings, Dangote ya bayyana kwarewa da kwazon Wigwe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Dangote ya ce:
“Domin tunawa da abokina, ɗan’uwana kuma dalibina, yanke shawarar sanya wa babban titin matatar mu mai kilomita 120 sunan Herbert Wigwe.
"Mutane za su rinka tururuwar nemo labarin Herbert Wigwe a duk lokacin da suka ga sunansa a kan babbar hanyar."
Iyalan Wigwe sun mutu ne tare da tsohon shugaban kungiyar canji ta Najeriya, Abimbola Ogunbanjo.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da Herbert Wigwe
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa an haifi Herbert Wigwe a jihar Oyo a ranar 15 ga watan Agusta, 1966, kuma ya rasu ne ya na da shekaru 58 a duniya.
Wigwe ya kasance kwararre ne a fannin banki, tattalin arziki da alkinta kudi, wanda kuma ya yi ilimi mai zurfi a nan gida Najeriya da ma kasashen ketare.
Legit ta dauki lokaci, ta zayyano muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da marigayi Herbert Wigwe.
Asali: Legit.ng