Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Shari’ar Murja Kunya
- Shari'ar shahararriyar 'yar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya na ci gaba da daukar hankulan jama'a musamman a Arewacin kasar
- Tun bayan da hukumar Hisbah ta Kano ta kama Murja, ta gurfanar da ita gaban kotu, aka fara zargin ana fifita matashiyar
- Legit Hausa ta tattaro wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da shari'ar Murja har zuwa hukuncin kotun a yau Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - A yau kotun shari'ar Muslunci ta Gama PRP ta yanke hukunci kan shari'ar shahararriyar 'yar TikTok Murja Ibrahim Kunya.
Mai shari'a Nura Yusuf Ahmad ya nemi da a kai Murja zuwa asibiti don duba lafiyar kwakwalwarta kamar yadda Dala FM ta ruwaito.
Sai dai, tun lokacin da aka ce hukumar Hisbah ta Kano ta kama Murja, mutane ke ci gaba da tofa albarkacin bakin su, musamman yadda ta yi kaurin suna a TikTok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganganun jama'a sun kara yawaita bayan da aka samu rahoton cewa an fitar da Murja daga gidan gyara hali da aka kaita ajiya na wani lokaci.
Legit Hausa ta tattara wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da shari'ar Murja Ibrahim Kunya.
1. Murja ba ta amsa laifin da ake zargin ta aikata ba
Bayan da hukumar Hisbah ta Kano ta gurfanar da Murja a gaban kotu, aka kuma karanta mata laifukan da ake tuhumarta da su, ta karyata aikata su.
An tuhumi Murja da yada bidiyon badala, bata tarbiyyar jama'a kamar yadda wasu mazauna unguwar da take suka kai koke ga Hisbah.
Bayan kin amsa laifin, mai shari'ar ya tura ta zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu (yau) don ci gaba da shari'ar.
2. An fitar da Murja daga gidan gyaran hali, an samu sabani
Da farko, mai magana da yawun kotun ya ce ba su da masaniyar an saki Murja daga gidan yarin, saboda umarnin ajiyarta alkali ya bayar.
Amma da maganar ta fara yaɗuwa a cikin jama'a, kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano, Misbahu Lawal Kofar Nassarawa ya ce kotun da ta tura Murja gidan ce ta ce a fitar da ita.
Ado Fage ya kuma yin amai ya lashe, inda ya fitar da sanarwar cewa an fitar da Murja ne don gudanar da sabon bincike bisa yarjewar alkali.
3. Gwamnati na goyon bayan Murja, cewar mutanen Kano
Mutanen Kano da suka yi tsokaci kan zargin an saki Murja daga gidan yarin, sun ce akwai alamar sa hannun gwamnatin jihar a ciki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mustapha Abdullahi, ya ce:
"Tana tare da gwamnatin jihar mai ci a yanzu, kuma duniya ma ta samu da hakan. Sannan munga irin manyan mutanen da suka je wajenta a kotun, akwai lauje cikin nadi."
Wani dan kasuwa, Mu'azu Rabiu ya ce:
"Idan har gwamnatin jihar, wacce jama'a ke kauna a yanzu ta ce za ta goyi bayan yarinyar, to abun ba zai yi mata kyau nan gaba ba."
4. Har yanzu Daurawa ne shugaban Hisbah na Kano
Akwai rade-radin da aka yi yadawa na cewar Mallam Aminu Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah saboda an saki Murja.
Sai dai a zantawar Legit Hausa ta wata majiya a hukumar, an tabbatar da cewa Daurawa bai yi murabus ba, kuma ya shiga ofis ranar Litinin.
Daga bisani ne mataimakin kwamandan hukumar, Mujahid Aminundeen ya fitar da sanarwar ƙaryata jita-jitar.
5. Gwamnatin Kano ba za ta tsoma baki a shari'ar Murja ba
A yammacin ranar Litinin, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ya fitar da sanarwar cewa babu ruwan gwamnati a fitar da Murja daga gidan gyaran hali.
Dantiye ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta tsoma baki a shari'ar Murja ba, sabanin yadda wasu ke zargin ta da hannu a sakinta.
Kotu ta ba da umarni a yi wa Murja gwajin ƙwaƙwalwa
A safiyar yau Talata, Legit Hausa ta ruwaito cewa kotun shari'ar Muslunci da ke da zama Gama PRP a jihar Kano, ta ce za a gudanar da gwajin ƙwaƙwalwa ga Murja Kunya don sanin abin da ke damunta..
Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya ce take-taken Murja sun nuna akwai aljanu a jikinta ko kuma aikin kayan maye ne kawai.
Ahmad ya ce Murja za ta zauna karkashin kulawar likitocin ƙwaƙwalwa da hukumar Hisbah na tsawon watanni uku.
Asali: Legit.ng