Ga Kudi Ga Kyau: Budurwa Ta Saki Bidiyon Hamshakan Masu Kudi 150 da Ke Neman Matan Aure

Ga Kudi Ga Kyau: Budurwa Ta Saki Bidiyon Hamshakan Masu Kudi 150 da Ke Neman Matan Aure

  • Wata budurwa ta ja hankali bayan da ta wallafa sunayen hamshakan samari 150 da ke neman matan aure ruwa a jallo
  • Jerin sunayen wanda aka yi wa lakabi da 'jerin sunayen Malak', zai taimaka wa mata wajen neman mazan da za su aura
  • Sai dai sunayen maza daga kasar Masar ne kawai a jaddawalin, inda Malak (mawallafiyar) ta ce a can kasar ne ta hadu da mijinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A irin wani yanayi da ba kasafai ya ke faruwa ba, wata budurwa mai suna Malak ta saki sunayen wasu hamshakan tuzurai 150 da ke neman matan aure ido rufe.

Budurwar ta yi wa jerin sunayen take da "jerin sunayen Malak", sannan ta wallafa shi a shafinta na TikTok da yakinin zai taimaka wa mata wajen haduwa da mijin aure.

Kara karanta wannan

Zo ka nemi aiki: Dan Najeriya ya nemo kamfanin da ke biyan albashin naira miliyan 3 duk wata

Jadawalin Malak
Budurwa ta wallafa jerin sunayen wasu hamshakan maza masu kudi da ke neman matan aure ruwa a jallo. Hoto: Getty Images (a kula: An yi amfani da hoton don misali kawai)
Asali: TikTok

Bidiyon jadawalin Malak

Duk da cewa jerin sunayen na dauke da sunayen maza 'yan kasar Masar ne kawai, sai da budurwar ta ce ita ma a can kasar ta hadu da nata abokin rayuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yawa daga mabiyanta sun nuna mamaki kan yadda ta iya hada wannan jaddawali, inda wasu ke ganin mazan sun hada kyau da kudi, Legit ta ruwaito.

Duba bidiyon a kasa:

Yar Najeriya ta sha alwashin auren attajirin mai kudi

A baya mun kawo maku labarin wata budurwa da ke yawan magana a kafar watsa labari ta podcast wacce ta rantse sai ta auri attajirin namiji ko ana ha maza ha mata.

Budurwar ta ci wannan alwashin ne a kokarinta na gujewa rayuwar da iyayenta ke yi yanzu cikin talauci, a cewar ta 'sun yi kuskuren auren juna'.

Kara karanta wannan

"Himma ba ta ga rago": Dalibar Najeriya ta yi hijira zuwa turai, ta kama aikin noma gadan-gadan

Matashiyar 'yar Najeriya ta yi yakini da cewa soyayya ba za ta sa ta auri namiji ba ma damar ba shi da hannu da shuni.

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta cika shekara 30

A wani labarin, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa (Kannywood) da na Kudu (Nollywood) Rahama Sadau, ta saki wasu zafafan hotuna yayin da ta ke murnar cika shekara 30 da haihuwa.

An haifi Sauda a ranar 7 ga watan Disam, 1993 a jihar Kaduna, kuma tauraruwarta ta fara haskawa bayan fitowa a fim din Gani ga Wane a shekarar 2013.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.