Wata mata tayi yunkurin siyan mota da kudin jabu da ta buga a gidanta

Wata mata tayi yunkurin siyan mota da kudin jabu da ta buga a gidanta

Wata mata a kasar Jamus ta yi yunkurin sayar mota daga wani dilalin motocci a birnin southwestern da ke Kaiserslautern a ranar Juma'a da ta gabata da jabun kudi da ta buga a gidanta.

Matar da dauki damin kudaden €15,000 kimanin naira miliyan 6.7 zuwa shagon dillalin motocin da ke Kaiserslautern domin sayar mota kirar Audi A3 2013 amma hakar ta bai cimma ruwa ba domin 'yan sanda sun cafke ta.

Gana damfarar matar bai yi wuya ba domin tayi amfani da na'urar buga takardu na amfanin gida da ofisoshi ne wurin buga kudaden na bogi a cewar kafar yadda labarai na DW a kasar Jamus.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Yan sanda sun gano na'uarar buga takardu makare da kudaden bogi a gidan matar mai shekaru 21 da ke birnin Pirmasens da ke mile 21 kudancin Kaiserslautern.

'Yan sandan kasar Jamus (BKA) sun ce 'buga kudaden bogi da niyyar zuwa yin sayaya da shi a kasuwanni laifi ke da ka iya janyo wa mutum zaman gidan yari na a kalla shekara daya duk da cewa dai a yanzu ba a gurfanar da matar a kotu ba.

Rundunar 'Yan sanda ta ce kwararrun 'yan damfara na amfani da fasaha mai wuyan ganewa wurin buga kudin jabu amma wadanda ba su kware ba suna iya nemo kayayakin buga jabun kudin a intanet cikin sauki kuma ba a bukatar wani kwarewa.

Sun kara da cewa takardar kudi na € 50 (kimanin N20,250) ce takardar kudin da masu buga kudin bogi su kafi kwaikwayo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel