Abokai 5 Sun Mutu Lokaci Guda a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

Abokai 5 Sun Mutu Lokaci Guda a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

  • Wasu matasa biyar su ka rasu nan-take yayin da hadari ya rutsa da su a safiyar Lahadin da ta wuce
  • Wadannan bayin Allah ‘yan jihar Katsina sun gamu da ajalinsu ne a hanyar zuwa bikin daurin aure
  • Hadarin ya auku a hanyar Katsina zuwa Kano, tuni aka birne su kamar yadda musulunci ya tanada

Katsina - Wasu matasa biyar sun rasu a sanadiyyar hadarin mota da ya auku da su a hanyar zuwa daurin aure a makon jiya.

Legit ta samu labari cewa hadarin da ya yi matukar muni ya auku ne a hanyar birnin Katsina zuwa garin Kano a ranar Lahadi.

Da motar ta yi hadari a garin Tsanyawa, sai da ta tsallaka dayan gefen titi, sannan ta ka bugi wata mota mai dauke da kaya.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

Matasa Katsina
Matasan da su ka mutu a Katsina Hoto: @MSIngawa
Asali: Twitter

Jami’an tsaro sun dauko gawar mutane 5

Majiyar ta ce da ‘yan sanda su ka ciro su daga motar, an yi gaggawan kai su asibiti inda aka tabbatar da dukkaninsu sun rasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunayen wadanda su ka riga mu gidan gaskiyar sun kunshi: Fatihulkhayr Yahya, Bello Hamisu Safana da kuma Bashir Bala Sani.

Ragowar kamar yadda mu ka samu rahoto su ne: Muhammad Ingawa da Aliyu Umar.

Duka mamatan abokan juna ne

Matasan abokan juna ne da tun a makarantar sakandare, sun yi karatu a makarantar kimiyyar kwana ta Ulul Albab da ke garin Katsina.

Bayan shekaru shida su na tare, a shekarar 2011 su ka kammala karatun sakandare, a halin yanzu su na aiki a wurare dabam-dabam.

Wani wanda ya yi karatu tare da mamatan, ya fada mana abin ya faru a hanyar zuwa daurin auren abokinsu, Abdulraheem M. Dalhat.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama tsagerun 'yan bindiga a Zaria bayan sacewa da kashe mutane

...An yi jana'iza a Katsina

Malam Ahmad Abdullahi wanda ya halarci jana’izar Bashir Bala, ya bayyana mana cewa jama’a sun taru a wajen yi masa sallah.

An birne mamacin da kimanin karfe 5:00 na yamma a makabartar da ke unguwar Gidan Dawa da ke Katsina bayan jana'izarsa.

Mutanen da su ka sansu, sun yi wa Malam Bashir Bala da sauran abokansa shaidar kirki.

Malam Muhseen Gambo Lawal ya rubuta a shafinsa: “Ya Allah ka gafartawa Bashir (Bala) da sauran kannenmu da su ka rasu.”

Matasa za su rasa aikin yi

Bayan shekaru kusan 7, sai ga labari Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power da aka kawo domin matasa su samu abin yi.

Ana tunanin tsarin ya taimaka wajen rage yawan masu zaman kashe wando. Sai dai akwai zargin rashin gaskiya da cuwa-cuwa a lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng