Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Sama da mutane 24 ne suka rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa
- A kalla mutane 24 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon babbakewa da suka yi a hatsarin mota da aka yi a kauyen Gwamfai
- Babban mai bada shawara ga gwamnan jihar ya ce, abun ya faru ne yayin da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ke kan hanyarsa ta zuwa garin Gumel
- Ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a yayin da direban mota kirar Toyota ta haya, mai mazaunin mutane 18 ya kasa sarrafa motar
A kalla mutane 24 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon babbakewa da suka yi a hatsarin mota da aka yi a kauyen Gwamfai da ke karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.
Babban mai bada shawara ga gwamnan jihar a fannin yada labarai, Auwal Sankara, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce abun ya faru ne yayin da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ke kan hanyarsa ta zuwa garin Gumel.
Ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a yayin da direban mota kirar Toyota ta haya, mai mazaunin mutane 18 ya kasa sarrafa motar. Ya fito ne daga Jahun inda ya nufi kasuwar Shuwari da ke karamar hukumar Kiyawa. Ya abkawa wani mai siyar da fetur ne dake bakin hanya.
KU KARANTA: Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda
Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, wani ganau ba jiyau ba ya sanar da cewa motar ta ki sarrafuwar wa direban ne. A hakan kuwa ya fada wa dan bunburutun da ke kan hanya inda motar ta kama da wuta wanda hakan ya jawo konewar wadanda ke ciki.
Sankara ya kara da cewa, gwamnan da ya tarar da hatsarin yayin da yake hanyarshi ta zuwa Gumel, ya umarci shugaban karamar hukumar da ya tabbatar da cewa an tallafawa iyalan fasinjojin.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce har yanzu dai ba a gano silar lamarin ba kuma ba a riga an tantance wadanda suka babbake a cikin motar ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng