Bidiyon Shugaban Daliban Jihar Adamawa Da Dan Sanda Mai Gadinshi Ya Jawo Cece-Kucen Jama’a

Bidiyon Shugaban Daliban Jihar Adamawa Da Dan Sanda Mai Gadinshi Ya Jawo Cece-Kucen Jama’a

  • 'Yan Najriya sun yi martani bayan wallafa wani faifan bidiyo inda dan sanda ke gadin shugaban dalibai
  • Wannan lamari ya faru ne a jihar Adamawa inda mutane su ka soki 'yan sanda da zubar da mutuncinsu
  • Wani mai fashin baki a harkar tsaro ya ce ba laifin shugaban daliban ba ne illa na hukumar 'yan sanda

Jihar Adamawa – ‘Yan Najeriya da dama sun yi martani bayan ganin wani faifan bidiyo na shugaban daliban jihar Adamawa da dan sanda na gadinshi.

Wani mai fashin baki a harkokin tsaro, Deji Adesogan ya yi martani kan faifan bidiyon tare da caccakar hukumar ‘yan sanda, Legit ta tattaro.

An gano dan sanda na gadin shugaban daliban jihar Adamawa
Bidiyon Shugaban Daliban Jihar Adamawa da Dan Sanda Mai Gadinshi Ya Girgiza Intanet. Hoto: @DejiAdesogan.
Asali: Twitter

Waye ya wallafa bidiyon na shugaban daliban?

Deji ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce ko kadan ba ya ganin laifin shugaban daliban, ya fi ganin laifin hukumar ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babban mai laifi shi ne shugaban yanki na ‘yan sanda (DPO) da ke kula da wannan yankin da kuma kwamishinan ‘yan sanda.

Ya ce:

“Gaskiya, ba na ganin laifin shugaban daliban na jihar Adamawa don dan sanda na gadinshi, na fi ganin laifin DPO da kuma kwamishinan ‘yan sanda da ke kula da wurin.”

Martanin jama'a kan faifan bidiyon shugaban daliban

‘Yan Najeriya da dama sun yi martani kan wannan faifan bidiyo inda su ke kokwanton karimcin jami’an ‘yan sanda.

@real_stqinless:

“Idan wannan ya samu mukamin shugaban Najeriya akwai aiki.”

@Kanto43969876

“Ina son yin martani amma sai na duba yawan aikata laifuka a yankunan ku, nima ina bukatar mai gadi ganin yadda wadannan shugabannin daliban ke da alfarma a siyasa.”

@tariqq2:

“Ba ni da tabbas, amma ina ga bai saba doka ba saboda dole sai ka bi ka’idar neman dan sanda mai gadi kuma ba kyauta ba ne, ‘yan kwallo da mawaka su na irin haka.”

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Matashin Ango Ɗan Shekara 21 Ya 'Halaka' Amaryarsa Kan Rigimar Abinci

@JmoonJ_ :

“Shin su na biyan su ne a matsayinsu na shugabannin dalibai saboda wannan ya fara takama kamar irin barayin 'yan siyasar mu.”

@Sadiq_002:

“Matsalar na farawa ne daga kasa. Daga nan ake fara handame kudaden al’umma.”

@fecomnet2:

“Wannan laifin ‘yan sanda ne, idan sun san aikinsu, ai ba za su amince da zuwa can ba.”

Dalibin BUK Ko FUD: Wanne ne sahihin sabon Shugaban Kungiyar Dalibai, NANS

A wani labarin, Kwamred Umar Farouq Lawal daga Jami'ar Bayero University BUK dake jihar Kano yana ikirarin cewa shi ya zama sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya NANS.

Yayin da dan Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Usman Umar Barambu, ke ikirarin cewa shine ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.