Dan Jami'ar Bayero da Dan Jami'ar FUD: Wanne ne sahihin sabon Shugaban Kungiyar Dalibai NANS

Dan Jami'ar Bayero da Dan Jami'ar FUD: Wanne ne sahihin sabon Shugaban Kungiyar Dalibai NANS

  • Dan jami'ar Bayero BUK yana ikirarin shi ya lashe zaben zama shugaban kungiyar daliban Najeriya NANS
  • Hakazalika dan jami'ar tarayya Dutse yana ikirarin shine sabodan shugaban NANS
  • Kungiyar NANS mai hakkin gwagwarmayar kare hakkin daliban Najeriya ta rabu gida biyu

Abuja - Kwamred Umar Farouq Lawal daga Jami'ar Bayero University BUK dake jihar Kano yana ikirarin cewa shi ya zama sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya NANS.

Yayinda dan jami'ar tarayya dake Dutse, Usman Umar Barambu, ke ikirarin cewa shine ya lashe zaben.

Rikici ya barke tsakanin bangarorin kungiyar kare hakkin daliban biyu.

Wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa ya haddasa dage zaben daga makon jiya zuwa yau ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, 2022, rahoton Punch.

Sakamakon haka, kungiyar ta kira hira da manema labarai na gaggawa don sanar da al'umma halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Hotuna: Atiku Ya Yi Kus-Kus Da Yan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP A Gidansa Da Ke Abuja

Ku dakace karin bayani...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal
Dan Jami'ar Bayero Dake Kano Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya NANS
Asali: Facebook

Daliban Jami’a Sun Jefar da Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

A bangare guda, kungiyar dalibai na kasar nan baki daya watau NANS, tace ta soma tattaunawa domin shigar da karar gwamnatin tarayya a kotu.

Punch ta ce a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, kungiyar ta NANS ta shaida mata cewa ta na kokarin yin shari’a da gwamnati da Ministan ilmi.

NANS tafitar da wani jawabi na musamman ga ‘yan jarida a garin Abuja, bayan Malam Adamu Adamu ya yi kira ga dalibai suyi karar malamansu.

Shugaban NANS na kasa, Sunday Ashefon ya maidawa Ministan ilmin martani da cewa gwamnatinsa za a maka a kotu ba 'yan kungiyar ASUU ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel