Shahararrun Masu Kudin Duniya da su ka Rasa Dukiyarsu a Sanadiyyar Mutuwar Aure

Shahararrun Masu Kudin Duniya da su ka Rasa Dukiyarsu a Sanadiyyar Mutuwar Aure

  • Saboda bambancin dokoki da al’ada, mutuwar aure a kasashen ketare ta na zuwa da wasu wahalhalu
  • Sai an yi ta shari’a a kotu da kuma lissafin arziki da kadarorin da tsofaffin ma’auratan su ka mallaka
  • A wasu lokutan, mata su kan tashi da kaso mai tsoka ko kuma lamarin ya juya da zawarawan attajiran

An samu attajiran da aurensu ya wargaje a sakamakon dalilai da-dama, Punch ta kawo jerin wadanda su ka rasa dukiya mai yawa saboda saki.

Shahararrun Masu Kudi
Jeff Bezos da matarsa da aurensu ya mutu Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

1. Bill da Melinda Gates

Bill Gates ya dade da Melinda French Gates a matsayin matar aure, da sabani ya shiga sabaninsu, dole su ka rabu, sannan ta tashi da $100m a 2021.

2. Jeff Bezos da MacKenzie Scott

A shekarar 2019 da mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya rabu da MacKenzie Scot da su ka yi shekara 25 tare, ta samu $38.3bn daga hannun shi.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Dr. Dre and Nicole Young

Fitaccen mawakin nan Dr. Dre ya biya Nicole Young $50m har sau biyu yayin da aurensu ya mutu, ya biya kason kudin karshen ne a shekarar 2022.

4. Adele da Simon Koneki

Simon Koneki ta samu $171m a hukuncin da wata kotu tayi a birnin Los Angeles bayan ta raba jiha da mawakin birtaniyar nan watau Adele a 2021.

5. Madonna da Guy Ritchie

Mutuwar auren sarauniyar Pop, Madonna ya jawo ta biya mai gidanta $92m da alakarsu ta kare a 2008, arzikin Guy Ritchie ya karu da ya rabu da ita.

6. Mel Gibson da Robyn Denise Moore

Mel Gibson ya auri malaman jinya Robyn Denise Moore a shekarar 1981, a lokacin da su ka rabu a shekarun baya, rahotonni sun ce ya rasa kusan $425m.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

7. Michael Jordan da Juanita Vanoy

A 2006 ne Gwarzon NBA na Michael Jordan ya saki Juanita Vanoy, ‘dan wasan kwallon kwandon ya batar da $168m ban da $2.1m da ya yi asara a kotu.

8. Tiger Woods da Elin Nordegren

Ana zancen Tiger Woods da ya shahara da wasan Golf ya biya Elin Nordegren $100m bayan igiyar aurensu ta katse a lokacin da ya ke ganiyarsa a Duniya.

9. Steven Spielberg da Amy Irving

Auren Steven Spielberg da Amy Irving ya zo da abin ban mamaki domin daga baya matar ta ce doka ba ta san da aurensu ba, a karshe aka sake ta da $100m.

10. James Cameron da Linda Hamilton

James Cameron da Linda Hamilton sun shahara ne a Titanic da Terminator, yayin da aurensu ya zo karshe a 1999, Hamiltan ta tsira da dukiyar da ta kai $50m.

Bill Gates a Aso Rock

A watan Yuni ne rahoto ya fito cewa Shugaban Najeriya, Mai girma Bola Tinubu ya gana da Aliko Dangote da shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates.

Ziyarar ba ta rasa nasaba da Gidauniyar Bill Gates don neman hadin kai da cigaba a Nahiyar Afirka kamar yadda mai kudin ya dade ya na yi a kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel