‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Yahoo da Zargin Birne Jariri da Rai Saboda Neman Duniya
- Dakarun PHALGA sun hada-kai da ‘yan sanda wajen kama wasu da ake zargin ‘yan damfara ne
- An cafke ‘Yan Yahoo-Yahoo din ne bayan an zarge su da birne wani yaro a kusa da bakin ruwa a Ribas
- Yanzu haka an mika su gaban ‘yan sanda domin ayi binciken da zai kai su zuwa kotu ko gidan yari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rivers - ‘Yan sandan Najeriya na reshen jihar Ribas da hadin gwiwar Dakarun PHALGA sun cafke wasu ‘yan damfara da aka fi sani da ‘Yan Yahoo.
Rahoton da The Guardian ta fitar ya tabbatar da cewa ana zargin wadannan ‘Yan Yahoo-Yahoo da zargin birne jariri da rai a ruwan Andoni a Fatakwal.
Shugaban rundunar tsaro na PLGA, Victor Ohaji, ya shaida cewa ya samu labarin ‘yan damfarar su na yin surkulensu a bakin ruwan a ranar Larabar nan.
'Yan Yahoo sun je bakin ruwa
Rahoton ya ce Victor Ohaji ne shugaban jami’an tsaron da ke kula da yankin tsibirin na jihar Ribas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ko da Ohaji ya dauki mutanensa zuwa bakin ruwan, sai su ka iske ‘yan damfarar sun tsere, amma dai duk da haka zuwan na su ya yi matukar amfani.
Da aka bincika, sai aka fahimci alamun an birne wani abu a cikin karkashin kasa, yayin da aka haka ramin, sai aka iske an birne sabon jariri a ciki.
An sanar da 'Yan sandan Ribas
Kamar yadda ya fada, ya sanar da al’ummar da ke makwabtaka da yankin, sannan ya ankarar da babban jami’in ‘yan sanda na reshen Azikiwe a Ribas.
Daga nan ne sai dakarun na sa-kai da kuma rundunar ‘yan sanda su ka shirya domin kamp‘yan damfarar da ake zargi da kashe rai saboda abin duniya.
A sanadiyyar haka ne Vanguard ta ce aka ci karo da ‘Yan Yahoo din su na fitowa daga wani otel, ko da su ka yi yunkurin tserewa, sai jami’an su ka cafke su.
Binciken jami'an 'yan sanda
Yanzu haka an damke mutum 12 daga cikinsu, kuma an mika su gaban ofishin ‘yan sanda na Azikwe da ke jihar Ribas domin a gudandar da bincike.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Grace Iringe Koko ta tabbatar da lamarin da masu kare hakkin Bil Adama irinsu Prince Wiro su ka yi Allah-wadai da shi.
Yakin ECOWAS a kasar Nijar
A wata hira da aka yi da Hajiya Naja’atu Muhammad, ta soki gwamnatin Bola Tinubu kan yakin da ta ke shirin yi da Nijar, ta ce Arewacin Najeriya aka yaka.
Kawu Sumaila ya ce a kundin tsarin mulki, su Sanatoci ne ke ba shugaban kasa izinin yaki, zuwa yanzu ya ce ba a aiko da bukatar aukawa makwabtan ba.
Asali: Legit.ng