Matashin Da Ya Shafe Shekaru 29 Yana Neman Iyayensa Ya Ce Har Yanzu Bai Cire Rai ba
- Wani dan matashi dan Najeriya ya ce bai sake sanya iyayensa a idanunsa ba tun bayan rabuwarsu yana da wata biyar kacal a duniya
- Matashin mai shekaru 29 ya bayyana cewa har yanzu bai cire rai da cewa zai sake haduwa da iyayen nasa ba
- Ya ce mahaifinsa ma’aikacin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA) ne da ke Ilorin kafin a kore shi, wanda hakan ya tilasta masa komawa Legas
Wani dan Najeriya, Adewole Idowu Oluwatobi, ya bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da neman 'yan uwansa da ya shafe shekaru 29 bai hadu da su ba.
A wani dogon sako na musamman da ya aikowa Legit.ng, matashin mai shekaru 29 ya ce ya rabu da iyayensa da ’yan uwansa uku sakamakon rabuwar da mahaifan nasa suka yi tun yana dan wata biyar a duniya.
Ya ba da bayanan danginsa da ya rabu da su tun yana karami
Ya bayyana sunan mahaifinsa da Adefalu Adewole da ’yan uwansa Monday, wanda shi ne babba, da kuma Taiwo da Kehinde, wanda suka kasance tagwaye.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Idowu, mahaifiyarsa mai suna, Adeyemi Funke, ta fito daga Kabba da ke jihar Kogi, mahaifinsa kuma dan asalin Ilaro ne da ke jihar Ogun.
Ya kara da cewa iyayen nasa sun rayu ne a gidan mai lamba 23 dake titin zuwa Abeokuta a Alakija, daidai tashar motar Mushin Olosha da ke birnin Legas a shekarar 1987.
Ya kuma bayyana yadda mahaifinsa ya fara kasuwancinsa mai suna 'Adesco Electrical Works' a Legas bayan ya barin aikin na ma'aikatar NEPA da ya yi.
Tun da ya fara tasowa yake ta fatan haduwa da iyayensa
Matashin ya ce tun tasowarsa yake ta faman neman iyayen nasa da 'yan uwansa, amma har yanzu dai ba wani bayani.
A cikin sakon da ya aikowa Legit.ng tare da hoton iyayen nasa, Idowu ya ce babban burinsa shi ne ya gan shi tare da iyayensa saboda shi ma ya ji yadda ake ji.
Ya kuma ce ba ya bukatar komai daga garesu illa kawai ya gansu a tare, sannan kuma ya yi fatan cewa mutane za su ci gaba da yada wannan sakon nasa har ya isa ga iyayen nasa.
Matashi ya hadu da malamarsa ta firamare bayan shekara 15, bidiyonsu ya yadu a Intanet
Wani labari da Legit.ng ta wallafa muku a baya, kun ga yadda rayuwa ke sauyawa, yayin da wani matashi ya dora biyonsa da malamarsa ta Firamare da ya shafe shekaru 15 bai hadu da ita ba.
Masu amfani da kafar Tiktok sun tafka muhawara kan bidiyon da ya dora hade da wani hoto da suka dauka shekaru 15 da suka gabata.
Asali: Legit.ng