"Ta Kara Kyau": Bayan Shekara 15 Matashi Ya Hadu Da Malamarsa Ta Firamare, Bidiyon Ya Bayyana

"Ta Kara Kyau": Bayan Shekara 15 Matashi Ya Hadu Da Malamarsa Ta Firamare, Bidiyon Ya Bayyana

  • Wani bidiyon TikTok ya nuna wani matashi tare da wata mata wacce malamarsa ce lokacin yana firamare a shekarar 2008
  • Wani mai amfani da TikTok, JJ Bravo ya sanya wani bidiyo wanda ya nuna wani tsohon hoto da ya ɗauka da malamar a shekarar 2008
  • Sun sake haɗuwa a shekarar 2023 inda suka ƙara ɗaukar hoto, amma ƴan TikTok sun gano wani abu na musamman dangane da kyawun malamar

Wani bidiyo ya nuna wani matashi tare da malamarsa wacce ta koyar da shi shekara 15 da suka wuce.

Matashin mai suna, JJ Bravo ya sanya bidiyon wanda ya nuna shi tare da malamar tasa yayin da aka ɗauke su hoto.

Matashi ya hadu da malamarsa ta firamare
Bayan shekara 15 sun sake haduwa Hoto: @Mr.bravo_o.
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, JJ Bravo ya nuna wani tsohon hoto da ya ɗauka tare da malamar a makarantarsu a shekarar 2008.

Kara karanta wannan

“Ina Matukar Kaunarsa Da Dukkan Zuciyata”: Matashiya Ta Wallafa Hotunan Sauyawar Mijinta Mai Nakasa Bayan Shekaru 10

Tsohon hoton ya nuna JJ Bravo sanye da kayan makarantarsa, goye da jakar makarantarsa a bayansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wancan lokacin malamar ta fi shi tsawo, amma yanzu JJ Bravo ya girma kamar yadda ya nuna a hoton da suka ɗauka a 2023. Malamar ta sa ita ma kyawunta ya ƙara bayyana, wanda ya ninka wanda ta ke da shi a baya.

Masu amfani da TikTok sun lura da kyauwunta inda suka ce a yanzu tafi kama da matashiya saɓanin yadda ta ke a shekarar 2008.

An rubuta a jikin bidiyon cewa:

"Malamata a firamare a yanzu da kuma a da."

Ƴan TikTok sun yi tsokaci akan bidiyon

Bidiyon da JJ Brown ya sanya ya ɗauki hankulan masu amfani da TikTok waɗanda suka yi faɗin kalamai masu daɗi akan su. Da yawa sun ce malamar ta fi kyau a yanzu saɓanin shekara 15 da suka gabata.

Kara karanta wannan

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

@Mafisisacco ya rubuta:

"Wai tana da saurayi ne?"

@Hindovei Maada Idriss ya rubuta:

"Md kake ci ne da ya sanya ka yi tsawo haka?"

@kaywhip ya rubuta:

"A gaskiya yanzu ta fi kyau. Shekarunta kamar raguwa suka yi."

Nakyanzi Sharon27 ta rubuta:

"Eh da gaske ne malamai basu tsufa."

Matashi Ya Sha Damfara Wajen Budurwa

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka bayan wata budurwa ta yi masa yaudarar bazata.

Budurwar dai ta sanya matashin ya tura mata kuɗi da sunan za ta zo wajen shi, amma sai ta yi muƙus kawai bayan ta karɓi kudaɗen.

Ya bibiyeta domin jin ko meyasa hakan ta faru kawai, sai ta goge shi gaba ɗaya ta yadda ba zai iya ƙara tuntuɓarta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel