Masu Amfani da A.A Rufai Wajen Barkwanci Su Na Fuskantar Barazanar Kurkuku
- An dauki mataki domin a daina wasa da hankalin Ahmad Lawan Rufai ko a kira shi da Bill Gates
- Barista Abba Hikima ya ce za su kafar wando daya da masu tunzuro matashin da sunan ana wasa
- Likitocin sun tabbatarwa Lauyan cewa tsokano A. A Rufai yana kara masa ciwon da yake damunsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Ahmad Lawan Rufai wanda aka fi sani da A.A Rufai ko a kira shi Bill Gates ya shahara a halin yanzu a kafofin sadarwa na zamani.
Barista Abba Hikima Lauya ne a garin Kano, ya yi magana a dandalin Facebook cewa doka za tayi aiki a kan masu tunzura wannan mutumi.
Lauyan ya ce sun dauki matakin ne da likitoci su ka shaida masu lallai ciwon A. A Rufai na karuwa a sakamakon abubuwan da ake yi masa.
A matsayin mai kare hakkin Bil Adama, Hikima ya sha alwashin tsayawa Bill Gates, ya ce babu wanda zai bari a rika wulakanta ‘danuwansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yanuwan AA Rufai sun koka
Da farko ana yawo da bidiyon A.A Rufai a dandalin sadarwa na zamani a matsayin abin ban Dariya, kafin gano ainihin larurar da ke damunsa.
‘Yanuwan Ahmad Lawan Rufai sun tabbatar da yana fama da matsalar kwakwalwa tun yana yaro, hakan ya jawo yake yawan sambatun kudi.
Matsayar Abba Hikima esq
“Jiya bayan wasu bayin Allah sun kai shi asibiti, likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake yiwa Lawan Rufai (Alhaji Rufa’i) tana kara tunzura shi. Kuma hakan na kara masa rashin lafiyar dake damun sa.
Saboda haka duk wanda ya kara tsokana ko tunzura wannan bawan Allah, sai mun dauki matakin shariah a kan sa ko waye Insha Allah.
Wannan rashin tsari ne da sanin ya kamata. Inda dan’uwan masu yin hakan ne babu wanda zai bari a dinga wulakanta shi haka. Sai kace ba musulmi ba?
Allah ya ba shi lafiya. Ameen."
- Abba Hikima
Likita ya yi Allah wadai
Wani likita ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa abin da ake yi wa wannan mutumi sam bai dace ba, za a iya daukar shi a matsayin cin zarafi.
Dr. Mohammed Al-Qasim ya ce daga ganin A. A Rufai za a iya zargin ya na da larura, ya ce abin da ya dace shi ne a zauna da shi ko ‘yanuwansa.
Sai an yi bincike tun daga dauko tarihin cutarsa, sannan za a iya gane halin da yake ciki, idan ta kama sai a hukunta masu wasa da hankalinsa.
Abin da yake faruwa a makwabta
Idan aka koma bangaren siyasa, za a ji labari cewa Abdullahi Aminu Shagali PhD yana cikin zababbun Kwamishinonin Gwamnatin Jihar Kaduna.
Watakila Ibrahim Hamza da Umma Khultume Ahmed su koma kan kujerunsu, su zama abokan aikin tsohuwar Akanta Janar Shizzer Nasara Bada.
Asali: Legit.ng