Budurwa Ta Nuna Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11, Bidiyon Ya Yadu
- Wata budurwa ta koka kan yadda ta shafe shekaru 11 ta na soyayya amma babu abin da saurayi ya mata
- Budurwar ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta nuna iya abin da saurayin ya saya mata guda uku
- Ta ce tsawon wannan shekaru abu uku kawai ya ba ta kyauta da suka hada da buroshin goge baki da man kai da kuma safa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata budurwa ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta bayyana abubuwa uku da saurayinta ya taba ba ta tsawon shekaru 11, Legit.ng ta tattaro.
Budurwar mai suna @manjaji0 ta wallafa bidiyon inda ta nuna buroshin goge hakora da safa da kuma man kai a matsayin abin da ya taba ba ta.
Budurwar ta nuna kyautar da saurayin ya mata a shekaru 11
“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta
A cewarta:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Bayan shafe shekaru 11 muna soyayya, a karshe na mayar masa da dukkan abin da ya siya min."
Ku kalli faifan bidiyon a kasa:
Faifan bidiyon ya yadu inda mutane da dama suka bayyana ra'ayinsu da kuma kaduwarsu akan lamarin.
Mutane sun yi tsokaci akan bidiyon budurwar
@Lemmy Motaung:
"Za mu iya ganin shi saboda kada mu yi soyayya da shi."
@Maleka Olebogeng Mor:
"Kin tabbata shekaru 11 ne ba mintuna 11 ba?"
@Snobza:
"Gaskiya ya kamata mu zauna da'ya'yanmu mata mu yi magana."
@Nondumiso Mhlongo:
"Hah wani ya ce a wallafa hotonsa don mu guje shi."
@queent070:
"Ba na dariya."
@Me and MissK:
"Haka ba zai taba yiyu ba, na ji wani iri."
@Mmatebello Serathi:
"Ban so na yi dariya ba, amma shi ne abin da ya kawo miki a shekaru 11?"
@lulu:
"Yanzu kin ajiye shi kenan har shekaru 11."
@yaxym:
"Ranar zagayowar haihuwa 11, Ranar masoya 11, Kirsimeti 11, Ranar mata 11, Ranar iyaye 11. Yoh."
@Ashley:
"Kanwata me kike yi har shekaru 11 kina soyayya."
@CandyPronto16:
"Wani ya taimaka ya fadamin cewa wannar raha ce."
Mercy Aigbe Ta Bayyana Darasin Da Ta Koya A Aikin Hajji A Makka, Ta Wallafa Bidiyo
A wani labarin, shahararriyar 'yar fim a Najeriya, Mercy Aigbe ta bayyana irin darussan da ta koya yayin aikin hajji.
Mercy wacce ta wallafa faifan bidiyo tare da mijinta, ta ce a Makkah babu bambanci tsakanin mutane.
Ta kara da cewa tsakanin talaka da mai kudi, tsoho da yaro da kalar fata ko jinsi duk daya ne a wurin Allah.
Asali: Legit.ng