Rikita-rikita Yayin Da Fasto Ya Ki Mayar Da Kujerar Haya Bayan Ya Gane Ta Na Tayar Da Matattu, Ya Sha Suka

Rikita-rikita Yayin Da Fasto Ya Ki Mayar Da Kujerar Haya Bayan Ya Gane Ta Na Tayar Da Matattu, Ya Sha Suka

  • Wani Fasto ya bayyana yadda wata kujera mai abin mamaki ta tayar da matacce bayan an daura shi a kanta
  • Faston M. Agochukwu da ke Fatakwal ya bayyana haka ne bayan mahaifiyar yaron ta zo neman addu'a
  • Ya ce bayan rashin nasarar samun shi, ta daura yaron akan kujerar da 'Apostle' ya zauna, kawai yaron ya tashi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mai bushara a majami'ar Shekinah da ke Fatakwal, M. Agochukwu ya rikirkita intanet bayan ya bayyana wata kujera da ke tayar da matacce.

Mai busharan ya ce kujerar da Manzo Johnson Suleman da aka karba haya ya zauna ya saye ta don ci gaba da dawo da matattu.

Fasto ya ki mayar da kujerar haya bayan gano tana tayar da matacce
'Apostle' Johnson Suleman Akan Kujerar Baiwa. Hoto: Gospel Agochukwu.
Asali: Facebook

Ya ce dole ya sayi kujerar saboda ta dawo da dan wata mambar majami'arsa, kamar yadda majiya ta bayyana.

Ya kara da cewa, makwabciyarsa 'yar kasar Ghana ta zo majami'arsa da mataccen yaronta wanda an yi magani har an gaji.

Kara karanta wannan

Ahir dinku: Tinubu ya dagawa Turawa EU yatsa kan rahoton zaben 2023, ya caccake su

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun yi ta bata shawarar binne yaron amma taki, ta kira wayan Faston a kashe, sai ta daura yaron akan kujera bayan ta yi addu'a, kawai yaron sai ya yi atishawa ya tashi.

Faston ya bayyana yadda kujerar ta tayar da matacce

A cewarsa:

"Ba ta da wani zabi da ya rage tazo majami'ar mu don yin addu'a, amma ta kira lamba ta a kashe.
"Bayan ta yi addu'a sai ta daura yaron akan farar kujerar da Manzo Johnson Suleman ya zauna, kawai yaron ya yi atishawa ya tashi."

Ya ce bayan ya dawo ya samu labari, bai mayar da kujerar ba kawai sai ya biya kudinta.

Mutane da dama sun yi martani akan wannan lamari.

Achebe Grace:

"Ka je ka mayar da kayan mutane idan baka biya ba, kana karya don samun mambobi a majami'ar ka. Mutane ne suke yarda da irin wannan, na tausaya saboda suna son irin wannan labarin."

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Aroo Ibra:

"Yaudara, yara nawa suka tayar a Najeriya? Karya ne, ta yaya mutum zai yarda da wannan labarin, ya kamata gwamnati ta fara kamasu, ka gwada haka a Amurka kaga idan baka je gidan yari ba."

Ọgbẹni Ajakaye:

"Ku nuna mana hotuna da bidiyo..wawayen mabiyanku ne za su yarda, ku sake rubuta wasan kwaikwayon."

Prince Alex Madojemu:

Ya kamata akai kujerar asibiti don warkar da mutane, ko a kyautar zuwa wani asibiti don warkar da mutane da dama."

Favour Mayor:

"Ba wannan ba ne ya ga sabbin kudi a cikin injila? Ina tare da kai baba, muje zuwa, kai kadai ne waliyyi yanzu."

Sweden: Fastoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani

A wani labarin, Fastoci a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a Sweden.

Fastocin sun bayyana cewa a shirye suke don su kare martabar Alkur'ani a ko wane lokaci.

Kara karanta wannan

“Na Nemi Uwar Mijina Ta Samo Mun Karamar Yarinya”: Matar Aure Ta Koka, Ta Saki Bidiyon Yarinyar Da Aka Kawo Mata

Sun roki Musulmi da kada su ce za su dauki wata fansa don bin koyarwar addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.