Ma’aikata, Dalibai Da ’Yan Kasuwa Sun Koma Hawa Kekuna A Maiduguri Bayan Cire Tallafin Man Fetur
- Cire tallafin mai a Najeriya ya jefa dubban mutane cikin wahala musamman abin da ya shafi karin kudin sufuri a kasar
- Tun bayan cire tallafin mai, mutane da dama a cikin manyan birane suka sauya daga hawa babura da motoci zuwa kekuna
- A birnin Maiduguri dalibai da ma’aikata har ma da ‘yan kasuwa sun koma hawa kekuna don ragewa kansu radadi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno – Wasu mazauna birnin Maiduguri da ke jihar Borno sun koma amfani da kekunan hawa don rage wa kansu radadin cire tallafin mai a kasar.
Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai din, ‘yan Najeriya suke cikin wani halin na tsadar man fetur.
Makwanni kadan da suka wuce babu kekuna sosai a titunan birnin, amma daga baya ko ina ka duba za ka ga masu kekuna daban-daban akan tituna.
Dalibai da ke zuwa makaranta da keke sun bayyana alfanun hakan
Daga farko abin dariya ne a gano mutum akan keke amma daga baya da sufuri ke kara tsada, ma’aikata da dalibai har ma da ‘yan kasuwa sun koma amfani da kekuna don biyan bukatunsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu amfani da kekunan sun shaidawa wakilin Daily Trust cewa amfani da kekunan ya rage musu wahalhalu bayan amfanin da hakan ke da shi ga lafiyarsu.
Wani dalibi mai suna Imam Kalli Imam wanda ke hawa keke zuwa Kwalejin Fasaha ta Ramat a kullum ya ce:
“Abin burgewa ne tuka keke zuwa makaranta, muna dariya da gaisuwa cikin jin dadi akan hanya da mutane da sauran dalibai daga gida zuwa makaranta.
“Ina jin dadin hakan, saboda ba zan bata lokaci ba wurin jiran mai tasi, kullum ina zuwa makaranta akan lokaci, ina jin kwarin gwiwa da kuma ‘yanci.
“Hakan ya sa dalibai ‘yan uwana suma suka fara hawa keke kuma suna jin dadin hakan.”
Jesse Adamu, wani dalibi ya ce yana hawa kekensa daga unguwar Customs zuwa makaranta nisan kusan kilomita hudu kenan.
A cewarsa:
“Ba ni da halin biyan kudin daki a makaranta, kuma kudin sufuri kullum karuwa ya ke, shiyasa na fara amfani da keke zuwa makaranta.”
Ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar muhalli ta jihar, Malam Bulama ya ce ya samu kwarin gwiwar hawa keke saboda sanin amfaninsa.
Ya ce:
“Ta na da amfani ga lafiya, kuma tana rage kashe kudade kan sufuri, mutane da dama yanzu sun koma hawa keke wanda zai rage yawan cututtuka na hayakin ababan hawa kuma hanyoyin mu da muhalli za su samu kariya.”
Masu gyara da siyar da kekuna a Maiduguri kasuwarsu ta bude bayan cire tallafi
Har ila yau, masu siyar da kekuna da masu gyara kasuwarsu ta bude tun bayan samun karuwar hawa kekunan a birnin.
Malam Abubakar Mohammed, wanda ya ke gyara da kuma siyar da keke da aka yi amfani da su ya ce yawan kwastomomi yanzu kullum karuwa yake, cewar rahotanni.
Ya ce:
“Kafin cire tallafi, ina iya wuni babu wanda yazo gyara ko siyan keke, amma yanzu duk kekunan da nake da su sun kare, ga shi kullum a cikin gyara muke, kwastomomi yanzu sun yi mana yawa.
FRSC Ta Shawarci 'Yan Najeriya Su Koma Amfani Da Kekuna
A wani labarin, Hukumar FRSC sun shawarci 'yan Najeriya su koma amfani da kekuna don rage radadi.
Kwamandan hukumar a jihar Bayelsa, Usman Ibrahim, ya shawarce su da su rike kekuna don karin lafiya.
Ya ce bayan rage kashe kudaden sufuri, tuka keke na kara lafiyar jiki da kuma kare muhalli daga hayakin ababan hawa.
Asali: Legit.ng