Makaho Da Ke Amfani Da Wayar ‘IPhone’ Ya Girgiza Intanet, Ya Ba Wa Makafi Shawara
- Matashi ya bayyana yadda ya tsinci kanshi bayan tsautsayin da ta mayar da shi makaho da bai hana shi komai ba
- Matashin mai suna Waziri Oluwatomi Ahmed ya ce matsalar ta same shi ne a 2019 yayin da yake aikin tuki
- Duk da haka bai cire rai a rayuwa ba, ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa kamar yadda sauran mutane suke
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani matashi mai suna Waziri Oluwatomi Ahmed wanda ya kasance makaho ya ba wa mutane mamaki yayin da yake iya amfani da wayar salula ta 'Android'.
Waziri ya ce wannan matsala ta faru da shi ne a shekarar 2019 inda ya rasa idonsa da hakoransa.
Amma duk da haka Waziri bai cire rai a rayuwa ba inda yake komai kamar yadda masu ido ke yi, a cikin wata hira da aka yi da shi, Waziri ya ce:
"Sunana Waziri Oluwatomi Ahmed, amma mutane suna kirana da Tomi Waziri, na yi karatu a jami'ar jihar Kogi, na karbi takardar shaidar karatu na bayan na makance."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Waziri makaho ya bayyana yadda abun ya faru da shi:
Abin ya faru ne a shekarar 2019 lokacin da nake tuki inda na hadu da wani mai kwacen waya da ya bukaci ya bashi wayar hannunsa.
Ya bayyana wa Legit.ng yadda abin ya faru:
"Na zama makaho shekaru hudu da suka wuce lokacin ina da shekara 27, ina cikin tuki don neman kudi saboda ni na saba da nema.
"A ranar 12 ga watan Satumba 2019, 'yan fashi sun kawo mini hari kuma suka harbe ni a fuska, sun tambayi na basu wayata.
"Na yi kokarin dauko wayar don na bashi, sai ya harbe ni, na yi sa'a da karamar bindiga ya harbe ni, hakan ya sa ta lalata min idanu da kuma karyewar hakora na."
Waziri ya bayyana yadda ya shiga damuwa bayan samun makanta, amma ya ce ya yanke shawarar mai da kanshi mai amfani ga iyalansa.
Ya bayyana yadda ya fara amfani da wayar 'Android'
Waziri ya ce:
"Ina tuna lokacin da na zama makaho, na yi tunanin zuwa makarantar makafi a Oshodi, a lokacin ne na samu karfin gwiwar fara mantawa da na samu makanta, amma na shawo kan damuwar da ke damu na.
"Ban taba sanin makafi suna amfani da wayar 'Android' ba da kuma na'ura mai kwakwalwa, lokacin ina makaranta ina sauraran wani yana amfani da wayar hannu da kuma karanta sakonni, abin ya ba ni mamaki."
Waziri ya ce daga ranar ya ji yana sha'awar koyar amfani da wayar salula, ya ce ya shafe makwanni uku don koyar amfani da wayar 'Android' a matsayinsa na makaho.
Waziri ya fadawa Legit.ng cewa yana amfani da wayar 'IPhone' da take da sautin murya a ciki wanda yake amfani da shi a wayar.
“Ta Ce Ba Za Ta Biya Ni Ba Har Sai Mun Yi Ido Hudu”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Masoyiyarsa Baturiya a Bidiyo
Ba Sauki, Amma A Haka Na Rene Su, Uwar Makafi 11 Ta Bayyana Yadda Take Sha Wahala Akan 'Ya'yan
A wani labarin, wata uwa wacce ta haifi yara 11 dukkansu makafi ta bayyana irin matsalolinta.
Matar mai suna Agnes Nespondi ta ce ta haifi yaronta na farko nakaho, ta yi tunanin daga nan shikenan.
Ta ce abin da yake damunta kullum shi ne idan ta mutu wa zai kula da su tunda daman ita kadai ke kula da su.
Asali: Legit.ng