An Gano Motar N55m a Delta Bayan Ɓarawo Ya Tsere da Ita Daga Hawa Ɗani Abuja

An Gano Motar N55m a Delta Bayan Ɓarawo Ya Tsere da Ita Daga Hawa Ɗani Abuja

Mohammed Manga ya bada labarin yadda su kayi da wani mai sayen mota da ya yi masu katuwar sata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

  • Shugaban kamfanin motocin Daggash Auto ya ce a wajen duba ingancin mota, aka dauke GLB 250
  • Farashin motar a kamfanin Mercedes Benz ya kai N55m, an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru

Abuja - Mohammed Manga ya samu kan shi a halin ha’ula’i bayan da wani da ake tunanin abokin ciniki ne ya tsere masa mota ta miliyoyin kudi.

Mohammed Manga ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya ce wani da aka sani da suna Henry, ya sace masu motar Marcedes Benz kirar GLB 250.

Wannan lamari ya faru a garin Abuja yayin da wani abokin kasuwancinsa ya zo da Henry wurin saida motocinsu da nufin yi masa ciniki mai tsoka.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Din Miliyan 12 Na Bogi Sannan Ya Tsere

Benz GLB 250
Motar Benz GLB 250 Hoto: @DaggashAutos
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan an kai mota ga wannan Bawan Allah da aka ce sunansa Henry, sai aka yi ciniki, aka amince a kan farashin da za a saida abin hawan.

Rahoton PUNCH Metro ya ce daga nan sai mai niyyar sayen motar ya bukaci a ba shi damar ya zagaya da ita domin jin lafiyar abin da zan saya.

Za a sha man fetur

A cewar Mohammed Manga, abokinsa ya shiga marsandin tare da Henry domin yin gwaji, daga nan sai ya nemi ya cire kudi saboda a kara fetur.

A lokacin da wannan mutumi ya fita daga motar domin zuwa shagon POS a unguwar Garki, kwatsam sai mai karyar niyyar sayen mota ya tsere.

Kamar yadda Manga yake fada, babu cunkoso a kan titunan Abuja, a haka aka sace marsandin da ake saida a kan fiye da Naira miliyan 50 a yau.

Kara karanta wannan

Tsaro: Bukarti Ya Barranta Da Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata A Dauka Akan 'Yan Bindiga

An sanar da hukuma da jama'a

Tuni ‘dan kasuwan ya sanar da sashen hana sace-sacen motoci na rundunar ‘yan sanda, ya fada masu launin motar da adadin tafiyar da ta sha.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na reshen Abuja, Josephine Ameh ta ce jami’an tsaro su na bibiyar motar da nufin a cafke wanda ake zargin.

Shugaban kamfanin motocin na Daggash Auto ya nemi taimakon al’umma a shafin Twitter, ya roki su sanar ta lambar waya domin samun la'ada.

An yi sa'a mota ta dawo

Ana haka ne sai rahotanni su ka zo cewa an gano wannan mota a jihar Delta, kuma ana tunanin an yi ram da wanda ake zargin ya dauke motar.

Sanarwar da aka bada a Twitter ta tabbatar da cewa an gano motar ne a garin Asaba a sanadiyyar yekuwar da mutane su ka yi a shafukan zumunta.

Za a fara shigo da motoci

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Alamu na nuna gwamnatin tarayya ta cire takunkumin da Muhammadu Buhari ya kakaba a baya na haramta shigo da motoci daga ketare da iyakoki.

Rahoto ya zo cewa ana sa ran matakin ya farfado da tattalin arzikin garuruwan da ke kan iyaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng