Hazikin Matashi Dan Najeriya Ya Sace Zuciyar Kyakkyawar Budurwa Cikin Minti 5, Hirarsu Ta Bada Mamaki

Hazikin Matashi Dan Najeriya Ya Sace Zuciyar Kyakkyawar Budurwa Cikin Minti 5, Hirarsu Ta Bada Mamaki

  • Wata hira da wani matashi ɗan Najeriya ya yi da wata budurwa a WhatsApp ta ɗauki hankula sosai a yanar gizo
  • Matashin dai ya tura mata saƙo a WhatsApp inda yake gaya mata dukkanin kadarorin da ya mallaka a duniya
  • A cikin ƙasa da mintuna biyar, budurwar ta yi martani kan saƙon da ya turo mata sannan ta amince ta zama budurwarsa inda ta yi ta yabonsa

Soshiyal midiya ta cika mamaki bayan bayyanar wata hirar WhatsApp a tsakanin wani matashi attajiri ɗan Najeriya da wata budurwa da ya gani yana so.

Matashin bai tsaya ba ta lokaci ba inda ya tafi kai tsaye ya gaya mata abinda ke zuciyarsa sannan ya gargaɗeta da kada ta tambayi wanene ya ba shi lambarta.

Matashi ya sace zuciyar budurwa cikin kasa da minti 5
Cikin sauri ta amince da soyayyarsa Hoto: Delmaine Donson, adamkaz / Getty images, Mediagist/ Instagram
Asali: UGC

A cikin hirar ta su ya fito fili ya gaya mata cewa son ta yake yi kuma ya sha ganinta ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.

Kara karanta wannan

"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Juna Biyu Ba Tare Da Kwanciyar Aure Ba": Matar Aure Ta Gaya Wa Kotu

Ya ci gaba da zayyano mata kadarorin da ya mallaka, inda ya gaya mata cewa yana da kuɗi, motoci biyu sannan yana son ta zama budurwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Barka da yamma sannan kada ki tambayi ya aka yi na samu lambarki. Bari na tafi kai tsaye: kina burgeni, na ganki sau da dama. Ina da kuɗi. Ina da motoci biyu. Ina son ki zama budurwata. Na ji labarin kina da saurayi, ki amince da soyayyata mu ga wanene zai fi kashe miki kuɗi."

A cikin ƙasa da mintuna biyar, budurwar ta amince ta yi soyayya da shi.

A kalamanta:

"Mai nasara, mai sarauta, zakaran gwajin dafi, zaki ya iso. Nzogbu nzogbu enyi mba enyi, tuo ya dike aahh. Na amince.”

Ƴan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakin su

@pere_juma ya rubuta:

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Ta Ki Bari Su Raya Sunnah

"Yauwa kun ga yadda ake samo soyayyar mace."

@ademola_x ya rubuta:

"Ko minti biyar ba a yi ba ta amince da gaggawa. Mata da kuɗi."

@collinsabiriba ya rubuta:

"Wannan ina ganin ita ce soyayyar da aka ƙulla cikin sauri wacce babu kamarta."

Matashi Na Neman Budurwar Da Za Ta Haifa Masa Yaro

A wani labarin kuma, wani attajirin matashi ɗan Najeriya na neman wacce za ta ɗauki ciki ta haifa masa yaro inda zai biyata ladan aiki har N20m.

Matashin ya bayyana cewa duk wata ɗawainiya zai ɗauketa sannan yaron ba a ƙasar nan za a haife shi ba. Ya ce zai biya rabin kuɗin aikin idan aka kammala ya cikasa sauran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel