"Ina Gane Matsalar Mota Daga Sautin Injinta": Makahon Da Ke Gyaran Mota A Abuja Ya Yi Bayani A Cikin Bidiyo

"Ina Gane Matsalar Mota Daga Sautin Injinta": Makahon Da Ke Gyaran Mota A Abuja Ya Yi Bayani A Cikin Bidiyo

  • Wani bakaniken mota da ya makance sama da shekaru ashirin ya bai wa wani mutum mamaki da basirarsa ta gyaran mota
  • Makahon da ke kanikancinsa a Abuja, ya ce zai iya gano matsalar da ke damun mota ta hanyar sauraron sautin injin kawai
  • ‘Yan Najeriya da dama da makahon ya birge sun ce yana buƙatar taimako, inda wasu suka yi ƙoƙarin janyo hankalin 'Guinness World Records' gareshi

Abuja - Wani mutum ya sha mamaki kan yadda wani bakanike makaho ya gyara masa motarsa, hakan ya sanya shi ɗaukar hoton bidiyonsa, ya kuma yaɗa a kafar sada zumunta ta TikTok.

Makahon ya ce ya shafe shekaru sama da 30 yana kanikanci, sannan ya kuma bayyana cewa shekarunsa 28 kenan a matsayin makaho, inda ya ce hakan ya faru ne a lokacin da yake tuƙa mota.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Fasinjoji Sauka Daga Jirgin Sama Bayan Ya Nemi Jakar Kilishinsa Ya Rasa, Bidiyon Ya Yadu

bakanike makaho ya bayyana yadda yake gyaran mota
Makahon bakanike ya bayyana yadda yake gyaran mota. Hoto: @anthonyejezie943
Asali: TikTok

Dalilin da ya sanya makahon ci gaba da aikin kanikanci

Bakaniken ya ƙara da cewa ya zaɓi ya ci gaba da kanikancin ne saboda shi ne hanyar samun na abincinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bakaniken makahon ya kuma bayyana cewa yana iya gane matsalar mota ta hanyar sauraron sautin injinta.

Ya ce idan ya ɗauki sifana, yana iya gane girmanta duk da lalurar da yake da ita ta makanta.

Mai motar ya ce bai fahimci cewa bakaniken makaho ne ba ne sai da ya gama gyara masa motar ta sa.

A cewarsa:

"Ina iya sanin matsalar mota ta hanyar sauraron sautin injinta, da zarar na riƙe sifana nake iya gane girmanta."

Kalli bidiyon makahon da ke kanikanci a Abuja a ƙasa:

Sharhin masu amfani da kafafen sadarwa kan bakanike makaho

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin sharhin da masu amfani da kafafar sadarwa ta TikTok suka yi kan bidiyon a ƙasa:

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Rayuwa Babu Ita Ba”: Dan Najeriya Ya Yi Wuff Da Tsohuwar Baturiya, Hotunan Su Yadu

Frankie_C ya ce:

"Allah ya ci gaba da yi wa mutuminnan albarka. Nakasasshe ne amma bai bari hakan ya hana shi ci gaba ba. Darasi a gare mu duka."

jibrilabubakar761 ma ya ce:

"Ko mu 'yan Najeriya za mu iya taimakon wannan mutumin."

official_profako ya ce:

"@Guinness World Records ku zo ku duba."

Onye Ujo Ebuna Mmanwu ya yi tambaya:

"A ina shagon nasa yake?"

Willjoedera Willjoe kuma ya ce:

"Ina da aboki makaho mai gyaran kwamfiyuta lokacin da muke makaranta, ikon Allah gaskiya ne."

RealRalph ya ba da shawara:

"Abinda wannan mutumin ke buƙata shi ne a yi masa aiki don dawo masa da ganinsa, shekarunsa na iya shafar ganin, amma ai yafi babu gaba ɗaya."

Emmanuel Mator927 ya ce:

"Ba kawai muna gani da idanunmu ba ne, idanu na ɗaya daga cikin abubuwan da ake gani da su.. Allah mai abin mamaki."

abdullahisani09 ya ce:

"@Guinness World Records fatan kun ga wannan."

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Abba Gida Gida ya magantu kan batun dawo da Sunusi Lamido kujerarsa

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa gwamnan jihar Kano, injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan makomar sabbin masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro.

Gwamnan ya bayyana cewa har yanzu bai gama yanke shawara ba dangane da matakin da zai ɗauka kan sabbin masarautun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng