Mata Ta Sayar Da Wayarta Ta Biya Wa Mahaifiyarta Tiyata Bayan Attajirin Mijinta Ya Ki Taimaka Mata

Mata Ta Sayar Da Wayarta Ta Biya Wa Mahaifiyarta Tiyata Bayan Attajirin Mijinta Ya Ki Taimaka Mata

  • Wata mata ta ce ta ji bakin cikin yadda attajirin mijinta ya ki taimakawa mahaifyarta don yi mata tiyata
  • Ta ce mjin nata yana da 'yan mata da yawa da yake taimaka musu da kudade da dama amma ita ko kwabo ba ya bata
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu yayin da wasu suka tausaya mata, wasu kuma ke cewa ta nemi hakkinta a kotu

Wata mata ta bayyana yadda ta siyar da wayarta don samun kudin da za a yi wa mahaifiyarta tiyata bayan mijinta ya ki taimaka mata.

Ta ce ta ji bakin ciki ganin yadda mijinta ke da makudan kudade amma sai dai ya kashewa 'yan waje ko kuma 'yan matansa na layi.

Matar ta ce attajirin mijinta ya ki taimakon mahaiyarta
Matar Ta Ce Tana Tunanin Rabuwa Da Shi. Hoto: @stockphoto.
Asali: Instagram

Matar wadda batason bayyana sunanta ta yada a wata kafar sadarwa ta Instagram, @couplestherapies don neman shawara.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Ta ce mijin nata ko kwabo ba ya bata amma yana kashe wa wasu kudi

Ta ce mijinta ya taba kashe naira miliyan 2.1 don taimakawa yayin bikin binne mijin wata mata, ya kuma siya mata wayar hannu da mota wadda ita kuma ko kudin bukatunta ba ya bata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewa ta roki mijinta ya taimaka mata da N380,000 don rashin lafiyar mahaifiyarta amma yaki, yayin da kuma ya kashewa budurwarsa N250,000 saboda bikin ranar haihuwarta.

Matar ta ce sai da ta siyar da wayarta don yi wa mahaifyarta tiyata

A cewarta:

"Na shiga yanayin bakin ciki. Na siyar da wayata don samun kudin yin tiyata ga mahaifiyata, amma na fadawa mijina cewa an sace wayar ne. Da naga zai yi bincike sai na fada masa gaskiya, yayin da ya ce zai kore ni a gida idan ban dawo da wayar ba."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Bayyana Yadda Aurensu Da Tsohon Mijinta Ya Mutu Cikin Watanni 7 Kacal

Ta ce ta kai karar sa zuwa wurin Fastonsu amma ya ki zuwa, inda wata mata a majami'ar ta ba ta kudin tiyatar da kuma shawartarta akan ta nemo hanyar da za tabi don zama da shi.

Ta kara da cewa:

"Na karbo wayar na bawa mijina, kuma bazan sake amfani da wayar ba har sai na siya da kudi na. Ina tsammanin na auri makiyi na, mutanen wannan gida kuba ni shawara ina son barin gidansa amma bana so mambobin majami'ar mu suce ban dauki shawararsu ba."

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke tausaya mata, wasu kuma cewa suke ta nemi hakkinta a kotu, wasu kuma sun bata shawarar ta yi addua don neman mafita.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane:

dear_onyinye:

"Ki yi hakuri da wannan jarabawar, auren mai kudi ba shi ne matsala ba, auren mai mutunci shi ne aure.

Kara karanta wannan

Yar Shekaru 13 Ta Kashe Miliyan N40 Da Iyayenta Suka Tara Wajen Buga Wasanni

@shanpepe:

"Ban taba yin aure ba don haka bansan shawarar da zan baki ba, amma idan barin auren ya fi a wurinki ki bari, saboda mambobin majami'ar ku ba su ne suke cikin auren ba.

@dezhenchard:

"Lokacin da kuka yi auren gargajiya ina dai 'yan uwanki ba su kuntata masa ba, saboda idan ya sha wahala komai kince sai ya siya to fa inaga wannan biyan bashi ne, wani lokaci ba ma son gaskiya."

Kauye Da Dadi: Wata Budurwa Ta Nadi Bidiyon Yadda Ta ke Wanka a Bandakin Tabo Ko Rufi Babu, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, wata budurwa ta wallafa faifan bidiyon yadda ta ke wanka a bandakin tabo a wani kauye.

Budurwar ta ce wannan shi ne karon farko da ta taba wanka a kauye musamman ta nadi bidiyon saboda ta yada shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.