Mehmet Ozyurek: Mutumin Da Ya Fi Kowa Dogon Hanci A Duniya Ya Yi Mutuwar Rashin Tsammani Yana Da Shekara 75

Mehmet Ozyurek: Mutumin Da Ya Fi Kowa Dogon Hanci A Duniya Ya Yi Mutuwar Rashin Tsammani Yana Da Shekara 75

  • Mutumin da yafi kowa dogon hanci a duniya ya mutu yana da shekaru 75 a duniya bayan kafa tarihi daban-daban
  • Mutumin Mehmet Ozyurek wanda dan kasar Turkey ne ya rike kambun Guiness World Record har sau uku a duniya
  • Ya fara samun kyautar wanda yafi kowa dogon hanci a duniya a shekarar 2001, sannan na karshe a shekarar 2021

Wani mutum da yafi kowa dogon hanci a duniya, Mehmet Ozyurek ya mutu yana da shekaru 75 a duniya.

Mehmet ya rike kambun ‘Guinness World Record’ har sau uku.

Marigayi Mehmet mai dogon hanci
Mehmet Kafin Rasuwarsa Yafi Kowa Dogon Hanci a Duniya . Hoto: GWR.
Asali: UGC

Mutumin wanda dan kasar Turkey ne ya samu kyautar kasancewa wanda yafi kowa dogon hanci a duniya, a maza, kuma wanda ya ke raye har sau uku.

A shekarar 2021 ne ya fara samun wannan kambu na ‘Guinness World Record’ a Los Angeles ta kasar Amurka, cewar Legit.ng.

Kara karanta wannan

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan a shekarar 2010 ma ya kara samu kambun a kasar Italiya da kuma na karshe a shekarar 2021.

GWR ta bayyana tsawon hancin Mehmet

Guiness World Record (GWR) ta tattaro cewa hancin Mehmet ya kai tsawon santi mita 8.8 wanda ya kai Inci 3.46 daga farkon hancin.

Daya daga cikin 'ya'yansa ya bayyana farin cikinsa

Baris ya ce:

“Ina matukar godaya ga mutanen Artvin da masoyansu, muna jin kunci, mahaifinmu mutum ne mai saukin kai, ba ya son yaga ya bata wa kowa rai.
“Mahaifina yana son hancinsa, kuma yana jin dadin rayuwarsa, ya taba fada mana a 2021 cewa “Yadda yake jin kanshi ya saba da na sauran mutane.
“Misali, idan muka shiga gidansa, zai fada mana irin abincin da suke girka wa.
“Duniya tana son hancinsa, Guiness World Record tana so, har matana ma tana so."

Kara karanta wannan

Hare-Haren Filato: Kungiyar CAN Ta Ba Wa Kiristoci Shawara Mai Muhimmanci

Mehmet da kanshi ya tabbatar yana son hancinsa a lokacin da yake raye

Ya ce duk lokacin da ya shigo wani wuri ko daki, hancin nasa na daukar hankalin mutane, amma bai dame shi ba ko kadan.

“Ina son hancina tabbas, wannan baiwa ce."

Mehmet ya ce yana jin dadi yadda ya zama daban a cikin mutane, duk da cewa mutane suna tsokanarsa.

“Abokaina suna cemin ‘Babban Hanci’ saboda su bata min rai.
“Amma ina duban kai na a madubi don in gane kai na. Allah ne ya yi ni haka, ba abin da zan iya yi akan hakan, na koyi yadda zan yi rayuwa cikin aminci a haka.”

'Yar Najeriya Ta Kafa Tarihin Lokaci Mafi Tsawo Da Aka Kwashe Ana Dafa Abinci

A wani labarin, wata shahararriyar mai girka abinci a Najeriya daga jihar Lagos ta kafa tarihi na wadda tafi kowa dadewa tana dafa abinci.

Budurwar mai suna Hilda Baci ta shafe akalla sa'o'i 87 da mintuna 45 tana dafa abinci daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel