"Gida Nake Son Dawowa" Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Koma Kasar Waje, Yana Neman Taimako Don Ya Dawo Gida

"Gida Nake Son Dawowa" Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Koma Kasar Waje, Yana Neman Taimako Don Ya Dawo Gida

  • Wani mutum ɗan Najeriya wanda ya tsallaka zuwa ƙasar Burtaniya, ya koma cizon yatsa kan komawar sa
  • Mutumin yace babu aikin yi a ƙasar inda yace ya nema har ya gaji bai samu ba, yanzu hanyar da zai dawo gida yake nema
  • Ya nuna katin sa inda yake cewa yana da makaranta a birnin Benin na jihar Edo, sannan yana mararin son ganin abokan sa

Wani ɗan Najeriga da ya koma Burtaniya ya koka kan cewa yana neman ɗaukin samun kuɗin da zai hau jirgi ya dawo gida domin yanzu kwata-kwata baya son zama a can.

Da yake tattaunawa da wata budurwa ƴar Najeriya cikin wani bidiyo a bakin titi a can Burtaniya, mutumin ya bayyana dalilin sa na rashin aikin yi a matsayin maƙasuɗin abinda ya sanya yake ƙwadayin dawowa gida.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

TikTok
"Gida Nake Son Dawowa" Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Koma Kasar Waje, Yana Neman Taimako Don Ya Dawo Gida Hoto: TikTok/@Jummyomolope
Asali: UGC

Ya koka kan cewa yayi neman har ya gaji amma bai samu aikin yi, hakan ya sanya ya yanke cewa babu aikin yi ƙasar.

Ya nunawa budurwar katin sa na musamman inda ya bayyana mata cewa yana da makaranta a Benin, babban birnin jihar Edo a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace ya na buƙatar fam ɗari biyar (£500) daidai da naira dubu ɗari biyu da tamanin da ɗaya da ɗari da ashirin da tara (N281,129), domin biyan kuɗin jirgin da zai dawo da shi gida.

"Ina so na koma Najeriya. Ina da makaranta a Najeriya. Nayi iyaƙar ƙoƙari. Babu aikin yi a UK." Inji shi

Ya bayyana cewa yana nan akan bakansa da ya samu kudin jirgi zai baro ƙasar, inda yake cewa yana son yaga abokanan sa na Najeriya.

"Bana son na cigaba da zama a nan." A cewar sa

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

Budurwar da tayi hira da shi itace ta sanya bidiyon a TikTok

Mutane sun cika da mamaki

Bidiyon wannan ɗan Najeriyan ya ba mutane matuƙar mamaki, inda suka yi ta yada maganganu. Ga kaɗan daga ciki:

SOMADYNA ya rubuta:

"Gwara ka tsaya a UK inda babu birkitattun mutanw sosai da ka dawo nan Najeriya inda kowa a birkice yake."

PeejayH2o ya rubuta:

"Wannan ƴan adawa sun kira shi kenan zuwa gida, sai ya dawo zai gane ashe shayi ruwa ne."

@Vincent ya rubuta:

"Ya je kawai ya shararawa wani bature mari, a kyauta za a dawo da shi gida."

"Bamu Ba Kai": Mutumin Da Ya Tsere Ya Bar Matarsa Da Da Tsawon Shekaru 33 Ya Dawo, Ya Nemi Wani Kason Gidansu

A wani labarin na daban kuma, wani mutum da yayi ƙaura shekara da shekaru ya bar iyalan sa ya dawo hannu Rabbana.

Bayan dawowar sa ya nemi wani kaso na daga cikin gidan iyalan sa, sun ce atafau yayi kaɗan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel