Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Yi Wa Dawainiya Ya Rabu Da Ita

Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Yi Wa Dawainiya Ya Rabu Da Ita

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya ta bayyana halin da ta tsinci kan ta bayan saurayin ta ya rabu da ita ba zato ba tsammani
  • Yayin da take ta sharɓar kuka, budurwar ta bayyana cewa ita ta ɗauki nauyin karatun sa zuwa ƙasar waje da kuɗin ta amma kawai ɓayan wata ɗaya sai ya sauya
  • Bidiyon na ta mai sosa zuciya ya ƴaɗu sosai inda ƴan yanar gizo suka ƙarfafa mata guiwa da kalamai masu taushi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna. Anjie ta sharɓi kuka bayan soyayyar ta ta tunkuyi ƙasa biyo bayan tafiyar da saurayin ta yayi zuwa ƙasar waje

Cikin karayar zuciya Anjie ta tambayi masu amfani da yanar gizo cikin wani bidiyo a TikTok, ko dama haka ɗabi'ar maza take.

Budurwa
Budurwar Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Yiwa Dawainiya Ya Rabu Da Ita Hoto: TikTok/Anjie_1
Asali: UGC

Matashiyar budurwar ta bayyana cewa ita ta ɗauki nauyin tafiyar sa zuwa ƙasar waje da ƴan kuɗaɗen da ta tara, amma kawai sai ya doɗe ta wata ɗaya bayan isar sa inda zai je.

Kara karanta wannan

"Zai Biya N10m Shigar Ciniki": Attajiri Dan Najeriya Na Neman Wacce Za Ta Haifar Masa Yaro, Zai Biya N20m

Ta bayyana a cikin bidiyon cewa ya doɗe ta ne bayan ya turo mata da saƙon ya rabu da ita. Budurwar dai ta kasa ɓoye baƙin cikin da take ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun ƙarfafa mata guiwa

Adriannamalik ta rubuta:

"Ka da ki ɗorawa kan ki laifi, ba kiyi kuskure ko kaɗan ba a abinda kika yi. Allah zai mayar miki da waɗanda suka fi su"

rghoto ta rubuta:

"Ƴar'uwata kada ki damu Allah zai baki ikon cin wannan jarabawar, kada ki damu da duk abinda wani daban zai ce, za ki tsallake wannan."

Adenike Adeoye98 said:

"Kina tambayar wai dama haka maza su ke? Omo iya mi, ina tunanin wannan ce soyayyar ki ta farko,, an karya miki zuciya kenan, to sannu."

Bakaniken Da Ya Mayar Da N10.8m Ya Bayyana Kudin Da Aka Bashi Matsayin Tukuici

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Tsakar Dare a Wata Jiha, Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta

A wani labarin na daban, wani bakanike da ya nuna halin a yaba ya bayyana tukuicin da ya samu bayan ya mayar da kuɗaɗen da aka yi kuskuren turo masa ta asusun ajiyar sa na banki.

Adadin kuɗin dai ya ba mutane mamaki sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel