Canza Naira: Jami’in Kula da Kudi a Jami’a Ya Mutu a Layin Banki Yana Neman Na Cefane
- Wani Bawan Allah mai suna Johnson Ademola Adesola ya rasu yana kokarin cire kudi a layin banki
- Marigayin ya kasance ma’aikacin Jami’ar LASU ne tun shekarar 1986, ya gamu da ajalinsa a banki
- Jami’ar jihar Legas ta tabbatar da rasuwar Johnson Adesola, ta kuma yi bayanin abin da ya faru
Lagos - Wani ma’aikaci a jami’ar jihar Legas wanda aka fi sani da LASU mai suna Johnson A. Adesola ya rasu a yayin da yake kokarin cire kudi a banki.
Rahoton da The Cable ta fitar a yammacin Talata ya tabbatar da cewa Johnson Adesola ya rasu ne a kan layin cire kudi a bankin Wema da ke cikin LASU.
Mista Adesola wanda aka samu labarin yana aiki a sashen kula da kudi na jami’ar ta Legas ya bar ofishinsa, ya kama hanya zuwa banki domin samun kudi.
Bayan ya kama layi ya fara bi, sai kwatsam wannan ma’aikaci ya fadi, daga nan aka ruga asibiti.
Asibiti sun ce ai har ya mutu
Rahoton ya nuna Adesola bai dade a layin cire kudin ba wannan abin ya faru a ranar Litinin, da aka je asibiti sai aka tabbatar ya yi ban-kwana da Duniya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da aka tambayi Mista Olaniyi Jeariogbe wanda shi ne shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na jami’ar LASU, ya tabbatar da rasuwar ma’aikacin.
"Kwarai, gaskiya ne. Kamar yadda duk mu ka sani, idan ajali ya yi kira sai an tafi. Mutuwa za ta iya zuwa mana a ko wani lokaci.
Shi (Adesola) yana cikin farfajiyar banki yana neman kudin da zai yi amfani da shi (ba na jami’a ba), sai mutuwar ta auko masa.
An yi kokarin ganin an ceto shi amma abin ya ci tura. Ba a taba sa ran faruwar haka ba, abin takaici ne.”
- Olaniyi Jeariogbe
Babban jami'in kula da kudi ya rasu?
Premium Times ta ce Jeariogbe ya karyata jita-jitan da ke yawo cewa babban jami’in da ke kula da harkar kudi a jami’ar ta LASU ya rasu, ya ce ba haka ba ne.
Kakakin jami’ar ya ce babban jami’in kula da kudi shi ne Mista Saheed Olayinka kuma yana da mataimaka hudu, dukkansu su na cikin koshin lafiya.
Johnson Ademola Adesola yana kula da sashen akawun, kuma shi mai kula da harkar kudi a tsangayar shari’a, ya fara aiki da LASU tun a shekarar 1986.
Sharrin miyagu ne - PDPPCC
An rahoto Darektan yada labarai a kamfen PDP a Ribas, Ogbonna Nwuke ya ce an wahalar da mutanen Najeriya, su na neman kudin da za su yi cefane.
A cewar 'dan siyasa, abin da mafi yawan ba su sani ba shi ne, miyagun da suka jawo wannan wahala sun yi da gan-gan ne saboda APC ta sha kasa a zabe.
Asali: Legit.ng