Meyasa Zata Yi Min Wannan Ɗanyen Aiki? Magidanci Ya Koka Kan Halin Matarsa

Meyasa Zata Yi Min Wannan Ɗanyen Aiki? Magidanci Ya Koka Kan Halin Matarsa

  • Bidiyon wani ɗan Najeriya da yayi arba da maƙudan kuɗade a ƙasan gadon sa ya ɗauki hankula
  • Magidancin yana shara ƙasan gadon sa ne kawai sai yayi kaciɓus da maƙudan kuɗaɗen
  • Magidancin ya koka kan yadda matar sa ta ajiye kuɗin a wajen ba tare da sanin sa ba

Wani magidanci ɗan Najeriya ya ga abinda ya ɗaure masa kai bayan ya gano cewa ya daɗe yana kwanciya a ƙasan maƙudan kuɗade ba tare da sanin sa ba.

Lamarin dai ya fara ne bayan abin da yake cajin waya da shi ya faɗa ƙasan gadon.

Magidanci
Meyasa Zata Yi Min Wannan Ɗanyen Aiki? Magidanci Ya Koka Kan Halin Matarsa
Asali: UGC

A ƙoƙarin ɗauko abin cajin, sai ya gano cewa ashe matar sa ta daɗe tana amfani da ƙasan gadon wajen yin ajiyar kuɗi, domin yayi arba da maƙudan kuɗade.

Abun cajin waya nake nema, ba wai da gangan na zo na buɗe wajen nan ba," A cewar sa

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Marasa Lafiya Na Shan Wuya, Magani Yayi Musu Wahalar Samu, Kungiyar Likitoci

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Magidancin ya ɗauki tsintsiya domin yin shara kawai sai yayi arba da maƙudan kudaɗen da aka ɓoye.

Ya share takardun kuɗi na N1000 da N500 waɗanda suka barbazu a ƙasan gadon.

Ba a san ko nawa ne yawan kuɗin ba domin bai ƙirga su ba. Sai dai ya fusata domin tsofaffin kuɗin yanzu sun daina aiki.

Ya kuma koka kan halin mata inda ya bayyana cewa ya sha tambayar ta rancen kuɗi amma sai ta kada baki tace masa bata da su.

Bidiyon ya ɗauki hankula sosai inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakin su akan abinda matar ta yiwa magidancin.

Ga kaɗan daga ciki:

@goldcristo ya rubuta:

"Ka adana kuɗin, bayan zaɓe za su cigaba da aiki."

@oliveruja ya rubuta:

"Shin matarka ba tana aiki ba? Ajiya take domin gudun ɓacin rana."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

@dharmey_trigger ya rubuta:

"Manta da cewa akwai kuɗi a ƙasan gadon ka, dattin dake wajen yayi yawa."

@agbonlanhor ya rubuta:

"Ka tafi CBN, kada ka watsar da su."

@eberelemoha ya rubuta:

"Ɗan'uwa kayi haƙuri, wannan matar ka ce ka cigaba da haƙuri kawai da halayyar ta.

Karancin Kudi: Dan Najeriya Ya Fito Da Tsofaffin Naira Da Aka Buga Shekara 15 Da Suka Gabata, Bidiyo Ya Yadu

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan Najeriya ya fito da tsofaffin kuɗin da aka daɗe da daina amfani da su.

Bidiyon ya ɗauki hankula matuƙa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel