Bayan Watanni 4 a Kabari, Mutumin China Ya Fadi Abin da Ya Jawo Ya Kashe Ummita
- Frank Geng Quangrong ya zayyanawa kotu yadda ya yi ‘kuskuren’ kawo karshen rayuwar masoyiyarsa
- Basinen da ake zargi da laifin kashe Ummukulsum Buhari yace yana kokarin kare kansa ne aka samu akasi
- Da aka je kotu ranar Alhamis, Frank Geng Quangrong ya nuna bai yi niyyar kashe wanda yake kauna ba
Kano - Mutumin nan na kasar Sin, Frank Geng Quangrong wanda ake shari’a da shi a kotun jihar Kano, ya fadi dalilinsa na aikata laifin da ake zarginsa.
Vanguard a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce Frank Geng Quangrong ya yi ikirarin hallaka Ummukulsum Sani Buhari domin ceton ransa.
Mista Frank Quangrong ya shaidawa kotu a zaman jiya cewa ya dabawa marigayiyar wuka ne ba tare da saninsa ba, a lokacin yana kokarin kare ran shi.
Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa
Mutumin da ake tuhuma da wannan laifi ya bayyana wannan ta hannun mai yi masa tafinta a shari’arsa da ake yi a gaban Alkali Sanusi Ado Ma’aji.
A hannun Ummukulsum Buhari ya karbi wuka?
Quangrong ya ce Marigayiya Ummukulsum Sani Buhari ce ta dauko wuta za ta caka masa, shi kuma sai ya yi maza ya karbe makamin daga hannunta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, bayan karbe wukar sai shi ya daba mata ba tare da ya sani ba, kamar yadda ya fada, a lokacin bai iya numfashi domin an shake wuyansa.
Kamar yadda Aminiya ta tabbatar da wannan magana dazu, wanda ake tuhuma ya nuna bai san halin da yake ciki ba a lokacin da ya aikata danyen aikin.
Duk abin da ya faru, Frank Quangrong ya ce bai san a ina ya soki Marigayiya Ummita da wuka ba, har sai da makwabcin ta ya sanar da shi da yake CID.
Akwai wani makwabci ga mai rasuwa mai suna Aminu wanda ya ziyarci Quangrong a lokacin yana tsare, ya fada masa yadda ya soke ta a kafada da kafa.
Sai bayan kwanaki 'Dan China ya ankara
Wannan mutumi ‘Dan Sin ya ce bayan kwanaki uku da yin abin ya ji shi ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Da samun wannan mummunan labarin, Basinen ya ce ya sharbi kuka domin bai da niyyar raunata Ummukulsum Buhari domin yana matukar kaunar ta.
An rahoto shi yana bada labarin yadda abin ya faru tirya-tiryan a dalilin kin daukar wayarsa. A karshe mai shari’a Ma’aji ya daga karar zuwa 7 ga Fubrairu.
'Dan China ya yi ikirarin kashe N60m
Da aka koma kotu a makon nan, an ji labari Frank Quanrong ya jero kudin da yake ikirarin ya kashewa Ummulkutum Buhari watau Ummita da suke tare.
Quanrong ya ce a lokacin da suke soyayya da wanda ake zargin ya kashe, ya ba ta jarin N18m, kuma ya saya mata gida, mota da wayoyi na miliyoyinkudi.
Asali: Legit.ng