Shugaban Yan Arewa Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Wike da Atiku a PDP

Shugaban Yan Arewa Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Wike da Atiku a PDP

  • Shugaban 'yan arewa mazauna kudu, Alhaji Saidu, ya roki gwamna Wike ya yi hakuri ya sasanta da Atiku Abubakar
  • Alhaji Musa Saidu, yace gwamna Wike yana da damar bayyana fushinsa kuma mutum ne mai karfin hango nesa
  • Shugaban yan arewa ya kuma gode wa Wike bisa Titunan da ya gina wa yan arewa mazauna jiharsa

Rivers - Shugaban kungiyar 'yan arewa mazauna kudancin Najeriya, Alhaji Musa Saidu, ya roki gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da tawagarsa G-5 su sasanta rikicinsu da Atiku Abubakar.

Alhaji Saidu yace gwamna Wike na da gaskiya ya nuna fushinsa kan abubuwan da shugabannin jam'iyya suka aikata masa amma lokaci ya yi da za'a yafi juna a fuskanci gaba, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Atiku da Gwamna Wike.
Shugaban Yan Arewa Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Wike da Atiku a PDP Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Ya jaddada cewa bai kamata aga Wike ko a kidaya shi cikin wadan da ke kokarin kai PDP kasa, jam'iyyar da ya zuba karfinsa da dukiyarsa wurin ginata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mr Quarong da ake zargi da kashe Ummita Yace Ya Kashe Mata Kudi Kusan Miliyan Sittin

"Gwamna Wike na da damar nuna fushinsa kuma ina yaba masa bisa yadda ya bayyana damuwarsa a fili babu boye-boye ba kamar wasu yan siyasa da zasu nuna kamar suna tare da kai amma zagon kasa suke maka."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wike mutum ne mai karfin hangen nesa, ina son a shawo kan batun Wike cikin kwanciyar hankali kuma ina kira ga gwamnan Ribas ya sulhunta da dan uwansa Alhaji Atiku Abubakar."
"Hakuri da yafiya ga juna yana da kyau a rayuwa, bayan haka muna mika godiya ga Wike bisa Titunan da ya mana."

- Alhaji Saidu.

Shugaban yan arewan ya kuma shawarci yan siyasa su yi takatsantsan da wasu sojojin gona dake nuna su wakilan yan arewa ne a Kudu, inda ya ayyana su da 'yan damfara.

Yace ya samu labarin wata tawagar wakilai ta ziyarci Chief Abiye Sekibo, jigon PDP a jihar Ribas. Ya bayyana cewa mutanen ba wakilan yan arewa bane a Ribas.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

Manyan yan takara na sahun gaba sun yi rashi a Oyo

A wani labarin kuma Mambobin PDP, APC da LP 2000 Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo

Kwanaki 43 kafin zaben shugaban kasa, Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi sun rasa dubbannin magoya baya a Oyo.

Yayin wani Ralin zagaye Tituna, mambobin APC, PDP da Labour Party sama da 2000 ne suka tattara suka koma Accord Party a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel