Munanan Bayanai Sun Bullo a kan Dalilin Cafke Mutumin Atiku da Aka Yi a Kasar Ingila

Munanan Bayanai Sun Bullo a kan Dalilin Cafke Mutumin Atiku da Aka Yi a Kasar Ingila

  • Bisa dukkan alamu hukumomin Birtaniya su na tuhumar Cif Raymond Dokpesi da tsohon laifin yin fyade ne
  • Raymond Dokpesi ya hau jirgin sama zuwa Ingila, amma yana isa tashar Heathrow, aka cafke shi
  • Jami’an tsaron kasar wajen sun yi karin-haske, sun ce ana binciken wanda aka kama ne bisa zargin fyade

United Kingdom - Jami’an ‘yan sandan Landan a kasar Birtaniya, sun shaida cewa su na binciken wani mutumi mai shekara 71 bisa zargin aikata fyade.

Punch ta ce a karshen makon jiya ne dakarun ‘yan sandan Landan su ka cafke Raymond Dokpesi a filin tashi da saukar jirage na Heathrow a Ingila.

Cif Raymond Dokpesi ya iso kasar Ingila ne ta birnin Frankfurt daga garin Abuja a ranar Lahadi, isowarsa ke da wuya, sai ya fada hannun jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Miyagun da Suka Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Fadi Abin da Suke Bukata

Shugabannin kamfanin DAAR Communications sun tabbatar da cewa Dokpesi ya hau jirgin Lufthansa zuwa Ingila ne saboda ana shirye-shiryen zabe.

Dokpesi yana tare da Atiku Abubakar

Gwamnatin Birtaniya ta gayyaci Atiku Abubakar, don haka Dokpesi wanda jigo ne a jam’iyyar PDP ya shiga cikin tawagar ‘dan takaran shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabin da ya fitar, Dokpesi ya godewa masoya da suka rika kwararo masa addu’o’i a lokacin da suka ji labarin ya shiga hannun hukuma a kasar waje.

Dokpesi
Raymond Dokpesi a Ingila Hoto: @ait_online
Asali: Twitter

Ana tuhumar mai shekara 70 da fyade

Punch ta tuntubi hukumomin kasar Ingila domin jin abin da ya sa aka tsare Dokpesi jim kadan bayan jirginsu ya sauka a filin Heathrow da ke Landan.

A amsar da aka samu, hukumomin ba su kama suna ba, amma sun ce ana binciken wani ‘dan shekara 71 ne da zargin ya yi fyade tun a Agustan 2019.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

Hukumomin sun ce an bada belin wannan mutum yayin da ake cigaba da yin bincike. Ana sa rai sai zuwa watan Afrilun shekarar nan za a cigaba.

“A sani cewa ba mu kama sunan mutumin da aka cafke, ba tare da an kai ga gurfanar da shi ba.”

- Hukumomin Birtaniya

Fyade kuma tsofai-tsofai da shi?

Da manema labarai suka yi yunkurin tuntubar dattijon a game da wannan zargi, ba a iya samun sa ba. Amma wata majiya tayi maza ta karyata wannan zargi.

Wani da yake aiki da wanda ake tuhuma ya ce babu yadda za ayi wannan Bawan Allah ya nemi yin fyade a lokacin da ya haura shekara 70 a kan doron kasa.

Fasinjojin jirgin kasa

Kun ji labari ana zargin 'Yan bindigan da suka shiga tashar jirgin kasa a Edo sun ce sai an biya N20m sannan mutane za su sake ganin ‘yanuwansa da aka sace

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Idan jami’an tsaro ba su yi gaggawar ceto wadannan mutane ba, kowa zai fanshi kan sa da N20m, kudin da ake ganin jama’a ba su da dalilin su a halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng