‘Dan Takaran APC Ya Shiga Uku, An Taso Shi Gaba da Zargin Kashe Mai Juna Biyu

‘Dan Takaran APC Ya Shiga Uku, An Taso Shi Gaba da Zargin Kashe Mai Juna Biyu

  • Wasu miyagun mutane sun kashe mai dakin Kalu Chima tana mai dauke da tsohon ciki a Ebonyi
  • Hadimin Gwamna David Umahi yana ganin kisan aikin Eni Uduma Chima da magoya bayansa ne
  • ‘Dan takaran na APC ya karyata Eze Panchris Ikechukwu, ya ce babu ruwan mutanen Ekoli Edda

Ebonyi - Eni Uduma Chima ya fito ya bayyana cewa babu hannunsa a kisan wata Baiwar Allah mai dauke da juna a yankin Ekoli Edda a jihar Ebonyi.

Leadership ta rahoto cewa Barista Eni Uduma Chima mai neman takarar ‘dan majalisa na yankin Afikpo ya musanya zargin da ake yi masa na kisa.

Uduma Chima yana takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya na shiyyar Afikpo ta Arewa da Afikpo ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

‘Dan siyasar yake cewa babu abin da ya hada shi ko wani daga cikin magoya bayansa da kisan da aka yi wa matar wani jami’in Ebubeagu a Amoso Eddah.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Ya Fada a Kan Kwankwaso da ya Ziyarci Jihar Abokin Hamayyarsa

Wasu miyagu suka kashe matar Kalu Chima ta na dauke da juna biyun watanni bakwai.

‘Dan takaran majalisar ya rike kujerar shugaban karamar hukumar Afikpo ta Kudu. Vanguard ta ce hakan ya jawo sabani tsakanin su da dakarun Ebubeagu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

yan sanda
Jami'an 'yan sandan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Gwamnati za tayi bincike a kai

A wani jawabi da Mai taimakawa Gwamnan Ebonyi a kan harkokin tsaro ya fitar, Hon. Eze Panchris Ikechukwu ya nuna da hannun Hon. Chima a mutuwar.

Hon. Eze Panchris Ikechukwu ya tabbatarwa mutane gwamnati za tayi bakin kokarinta wajen bankado wadanda suka yi wannan aiki domin a hukunta su.

Hadimin na Gwamna David Umahi ya yi tir da abin da ya faru, ya kuma ce ba za su bari a kauda tunanin hukuma daga binciken wannan mummunan kisa ba.

Ba aikin mutanen Ekoli Edda ba ne

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

A martanin da ya yi, ‘dan takaran 'dan majalisar ya ce zancen Mai ba Gwamna shawara na cewa aikin magoya bayansa da ake kira Ekoli ne, ba gaskiya ba ne.

Barista Eni Uduma Chima yake cewa mutanen Ekoli Edda ba za su kashe rai ba, sannan ya yi kira ga masu yada jita-jitar su guji abin da zai raba al’umma.

An rahoto Chima ya ce watakila Hon. Eze Ikechukwu yana fadan gaskiyar abin da ya sani ne amma a cikin jahilici domin bai da wani ilmin binciken laifuffuka.

A jawabinsa, ‘dan siyasar ya zargi dakarun Ebubeagu da tasa mabiyansa a gaba, ya ce abin takaici ne da kisan matar ya jawo aka hallaka wani Eseni Kalu Egwu.

Malamin tsibbu ya rasu otel

An ji labari wani sananne kuma gawurtaccen boka da ake kira Ejiogbe ya gamu da karshensa bayan ya nemi matar Fasto a garin Ikere-Ekiti a Jihar Ekiti

Kara karanta wannan

Shettima Ya Yabi Kwankwaso, Amma Ya Kwankwashi Kan Atiku da Peter Obi a Bidiyo

Malamin tsibbun ya mutu a ranar Litinin da ta wuce sa’ilin da ya gama lalata da matar malamin addini a otel, ana zargin tsafin da ke jikinta ya kashe shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng