Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa
- Aminu Adamu ya yi amfani da Twitter da ya sa shi a matsala wajen yin magana bayan samun ‘yancinsa
- Dalibin jami’ar ta FUD da ke jihar Jigawa ya ba Aisha Buhari hakuri, yana mai alkawarin zai canza halin
- Matashin yayi godiya ga wadanda suka tsaya masa, yace kaddarar da ta hau kan shi darasi ne a kan kowa
Jigawa - Aminu Adamu, matashin da ya shafe kwana da kwanaki a tsare a bisa zargin cin mutuncin Aisha Buhari, ya leko Twitter a karon farko.
Legit.ng Hausa ta bibiyi shafin wannan Bawan Allah da safiyar Ranar Lahadi, 4 ga watan Nuwamba 2022, bayan ya fitar da wasu jawabai a jiya.
Da kimanin karfe 10:30 na dare a ranar Asabar, Aminu Adamu wanda aka fi sani da Aminullahie a Twitter, ya fito yana ba daukacin jama’a hakuri.
Baya ga hakuri da ya bada musamman ga uwargidar shugabar kasar Najeriya, dalibin ya godewa duk mutanen da suka taimaka wajen kubutar da shi.
Jaridar Daily Nigerian ta fitar da rahoto cewa Adamu ya yi magana kan kaddarar ta auka masa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Nagode Mama
"Ina so in yi amfani da wannan dama, in bada hakuri ga duk wadanda na batawa rai, musamman mamarmu, Aisha Buhari
Ban yi niyyar in bata maki rai ba, kuma idan Allah ya so, zan zanza in zaman a kwarai. Nagode da afuwarki, nagode Mama.
Ina kuma so in yi amfani da wannan dama domin nuna godiya ta ga wadanda suka taimaka mani da na shiga mawuyacin hali
Babu wanda ya isa ya tserewa kaddar Ubangiji, amma ya kamata abin da ya faru da ni ya zama darashi ga kowanenmu.
Nagode gaba dayanku!"
A dalilin abin da ya faru, matashin ya samu shahara sosai a shafukan sada zumunta. A yanzu haka yana da mabiya fiye da 29, 000 a Twitter.
Maganar da ya yi, yana bada hakuri, ta zagaya sau fiye da 1200 a cikin kimanin sa’o’i 21.
Dalilin fito da Aminu
A karkashin jagorancin Kwamred Usman Barambu, an samu rahoto Daliban Najeriya sun yi niyyar zanga-zanga muddin aka cigaba da tsare Aminu Adamu.
Lauyan matashin yana ganin barazanar nan ce ta tada hankalin jami’an 'yan sandan kasar nan, har aka yi watsi da shari’ar zargin cin mutuci da ake yi masa.
Asali: Legit.ng