Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari

Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari

  • Lauyan da yake tsayawa Aminu Adamu ya bayyana abin da ya sa aka janye karar da ake yi a kotu
  • Festus Agu yana ganin barazanar Shugaban kungiyar NANS ta taimaka wajen hakura da shari’ar
  • NANS tace za a barke da zanga-zanga a fadin jihohi idan ba a fito da dalibin jami’ar ta FUD ba

Abuja - Jami’an ‘yan sanda sun janye karar da suka shigar a kan Aminu Adamu, bisa zargin cin mutuncin Uwargidar Najeriya, Aisha Buhari.

A wani rahoto na ranar Asabar, 3 ga watan Disamba 2022 da Premium Times ta fitar, an ji abin da ya kubutar da wannan dalibi mai karatu a jami’a.

Festus Agu wanda ya tsayawa dalibin a kotu, ya bayyana cewa an hakura da wannan shari’a ne saboda kungiyar daliban Najeriya ta tsoma baki.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

Kungiyar NANS mai jagorantar dalibai a kasar nan ta shirya fara gudanar da zanga-zanga a fadin jihohi domin bada kariya ga Aminu Adamu.

Kokarin Kwamred Usman Barambu

Shugaban NANS na kasa, Usman Barambu ya fitar da jawabi cewa daga ranar Litinin mai zuwa za a barke da zanga-zanga a dalilin tsare dalibin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Agu ya fadawa jaridar, an janye shari’a ne kwana daya bayan an ji za a shirya zanga-zanga domin a fito da matashin da ake kara.

Aminu Adamu
Aminu Adamu da Aisha Buhari Hoto: www.herald.ng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Kwamred Usman Barambu yana cikin wadanda suka fara ganawa da matashin mai shekara 24 bayan ya samu ‘yanci.

Watsi da karar da aka yi, yana nufin dalibai a karkashin inuwar NANS ba za su fita kan tituna ba. Watakila shi kuma dalibin ya iya rubuta jarrabawarsa.

Kowa ya yi hankali

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

Tuni mutane suka shiga maida martani biyo bayan abin da ya faru, wasu suna cewa ko a haka, matashin ya dandana kudarsa a hannun jami’an tsaro.

A gefe guda kuma wasu suna bada shawarar ya shigar da kara a gaban kuliya bisa zargin azabtarwa, cin zarafi da tsare shi da aka yi ba tare da ka’ida ba.

Zargin da ake yi masa shi ne amfani da Twitter ya ci zarafin matar shugaban kasa, bisa hakan ya aika laifin da ya sabawa sashe na 391 na ‘Penal code’.

Martanin Naja'atu Muhammad

A wata hira da aka yi da ita kwanaki, an ji labari Naja’atu Mohammed ta soki yadda Aisha Buhari ta dauki doka a hannunta a kan lamarin Aminu Adamu.

Ana zargin uwargidar shugaban Najeriyan ce ta bada umarni a cafke dalibin saboda ya ci mata zarafi da wasu maganganu da ya rubuta a shafin Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng