‘Yar Baiwa Daga Najeriya Mai Shekara 13 Ta Kafa Tarihin Shiga Jami’a a Kasar Amurka

‘Yar Baiwa Daga Najeriya Mai Shekara 13 Ta Kafa Tarihin Shiga Jami’a a Kasar Amurka

  • Emmanuella Mayaki wata ‘yar Najeriya ce mai shekara 13 da haihuwa da za ta fara karatu a jami’a
  • Wannan yarinya ta zama wanda ta fi kowa karancin shekaru a tarihin daliban jami’ar Amurka
  • Mayaki za tayi digiri a bangaren Komfuta da tayi fice a jami’ar Mary Baldwin a Birnin Virginia

United States - Emmanuella Mayaki, yarinya mai shekara 13 a Duniya, ta zama daliba mafi karancin shekara da aka dauka a jami’iar kasar Amurka.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace jami’ar Mary Baldwin a Amurka ta dauki Emmanuella Mayaki domin ta karanta ilmin komfuta a bana.

Mayaki ta samu damar karatun ne ta karkashin wani tsari na fitattun ‘yan baiwa a Duniya. A jarrabawar da aka shirya masu, yarinyar ta samu 91%.

“Ya Emmanuella, muna taya ki murnar daukar ki da aka yi a tsarin fitattun ‘yan baiwa a jami’ar Mary Baldwin! Barka da shigowa ajin PEG na 2026!”

Kara karanta wannan

Cire tallafin mai: Gwamnatin wata jiha ta rage ranakun karatu da aiki zuwa 3 a mako

- Takardar samun gurbi a Jami'ar Mary Baldwin

Malama tun a shekara 11

Tun tana ‘yar shekara 11 a 2020, wannan ‘yar baiwa ta kafa wata cibiyar karatu domin ilmantar da yara mata a kan ilmin kimiyyar ICT a garin Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Guardian tace Emmanuella Mayaki ta kafa makaranta mai suna ‘CodeKid’ domin taimakawa mata su san ilmin komfuta da makamantansu.

Emmanuella Mayaki
Emmanuella Mayaki Hoto: collegesofdistinction.com da www.naijablaze.com
Asali: UGC

Mayaki ta kafa makarantar a Najeriya bayan irin abin da ta gani a Birtaniya. Yanzu masu shekara 6 zuwa 15 suna koyon HTML, CSS, PHP da sauransu.

Tun ta na ‘yar shekara 11 aka dauke ta aiki a wata makaranta a Coventry. A 2022, an zabi wannan yariniya a matsayin gwarzuwar STEM a birnin New York.

Digiri a bangaren komfuta

Mayaki tana koyar da ‘yan makarantar firamaren ilmin komfuta, wannan ya sa a jami’ar Mary Baldwin za ta karanci wannan fage domin ta samu digiri.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Sowore ya bayyana sunayen abokan cin mushen Emefiele

Punch tace saboda sha’awar wannan fani, Mayaki tana yin kwas a irinsu SoloLearn da Udemy. A nan ne ta samu satifiket a HTML, PHP, CSS da kuma SQL.

Rahoton ya kara da cewa, baya ga haka, ta na da satifiket a JavaScript, JQuery, Python da Java. Dalilin haka, Mayaki ta samu kyaututtuka iri-iri a Amurka.

Sha'ain ilmi a Najeriya

Da fatar bakinsa, ba wani ne ya fada ba, kwanaki an ji labari Adamu Adamu ya soki kan sa, yana ganin bai yi abin kirki a matsayinsa na Ministan ilmi ba.

Dama can kafin a nada Adamu Adamu a 2015, wasu sun yi ta suka ganin cewa asalinsa Akanta ne wanda ya koma aikin jarida, ba masani a harkar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel